Rikicin Neman Zabe Ya Kare Tsakanin Mutanen Tinubu da Shugabannin Jam’iyyar APC

Rikicin Neman Zabe Ya Kare Tsakanin Mutanen Tinubu da Shugabannin Jam’iyyar APC

  • Gwamnonin APC, NWC da Shugabannin kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu sun yi wani taro
  • Atiku Bagudu yace sun shawo kan matsalar da ake samu tsakanin APC NWC da Kwamitin takaran 2023
  • Wani a kwamitin PCC ake zargi ya yi garajen fitar da sunayen ‘yan kwamitin takara kafin a gama aiki

Abuja - Jam'iyyar APC mai mulki tayi nasarar kawo karshen rigimar da ake tayi a dalilin kafa kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na 2023.

Rahoton da muka samu daga BBC Hausa a ranar Alhamis, ya bayyana cewa barakar da ke tsakanin Asiwaju Bola Tinubu da ‘yan majalisar NWC ta dinke.

Gwamnonin APC a karkashin inuwar PGF wanda Gwamna Atiku Abubakar Bagudu yake jagoranta, tayi wa ‘dan takaran da shugabanni na kasa sulhu.

Kara karanta wannan

An Sake Duba Sunayen Kwamitin Kamfen din Tinubu, Adamu ya ki Halarta

Atiku Abubakar Bagudu ya sanar da BBC Hausa sun magance matsalar da aka samu, yace an samu kuskure ne wajen fitar da sunayen kwamitin kamfe.

Za ayi wa Tinubu aiki a 2023

Gwamnan na Kebbi ya tabbatar da cewa shi da abokan aikinsa suna goyon bayan Bola Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

''Da ma wani kuskure aka yi, wato wani ma'aikaci ne ya fitar da jerin sunayen 'yan kwamitin yakin neman zaben kafin a kammala hadawa.
Ka san ana hada sunayen ne ana tuntuba. Amma yanzu an samu fahinta. Da ma ba baraka ba ce.
Shugabannin Jam’iyyar APC
Gwamnonin APC a taro da PCC da NWC Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Kuma dukkan mu muna jaddada goyon bayan ga shugabannin jam'iyyarmu da dan takaranmu na shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu."

- Atiku Abubakar Bagudu

Rahoton The Nation ya tabbatar da cewa kan jiga-jigan APC ya hadu a sanadiyyar kokarin da kungiyar PGF tayi wajen sasanta PCC da majalisar NWC.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar PDP Za Ta Kira Taron Gaggawa Domin Ceton Takarar Atiku Daga Watsewa

A karshen zaman, kowane bangare ya amince zai bada gudumuwarsa wajen ganin Asiwaju Bola Tinubu da Kashim Shettima sun kai labari a zaben 2023.

Gwamnoni, shugabannin jam’iyyar APC na kasa da kwamitin takaran Bola Tinubu sun amince a fito da tsarin da za a bi wajen sasanta duk wasu rigingimu.

Rikicin cikin gidan PDP

Ku na da labari cewa Jam’iyyar hamayya ta PDP tayi wani zama wanda ya yi zafi a ranar Talatar nan bayan dawowar Dr. Iyorchia Ayu daga kasar waje.

Ana jira Iyorchia Ayu ya yi murabus, sai ga shi ya bada umarni ayi bincike a kan mataimakansa a majalisar NWC da suka dawo da kudin da aka ba su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng