Tsohon Gwamnan Borno Ali Modu Sheriff Ya Yi Ganawar Sirri Da Obasanjo

Tsohon Gwamnan Borno Ali Modu Sheriff Ya Yi Ganawar Sirri Da Obasanjo

  • Tsohon gwamnan jihar Borno ya kai wata ziyara jihar Ogun, ya gana da tsohon shugaban Najeriya Obasanjo
  • Ana kyautata zaton ganawar tasu na da alaka da batun zaben 2023, duk da cewa bai yi magana kan haka ba
  • Ali Modu Sheriff ya kasance tsohon shugaban jam'iyyar PDP, a yanzu ya tsinci kansa a jam'iyyar APC

Abeokuta, jihar Ogun - Tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff ya yi wata ganawar sirri da tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obansajo.

Ganawar da aka yi a dakin karatun Obasanjo da ke Abeokuta a jihar Ogun an ce bata wuce ta mintuna 40 ba, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Jim kadan bayan kammala ganawar, tsohon gwamnan ya zanta manema labarai da ke neman sanin musabbabin ganawar.

Ali Modu Sheriff ya gana da tsohon shugaban kasa Olusegun Obansajo
Tsohon Gwamnan Borno Ali Modu Sheriff Ya Yi Ganawar Sirri Da Obasanjo | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ganawar ta su dai ana kyautata zaton ba zata rasa nasaba da zaben 2023 mai zuwa ba, kasancewar ya bayyana bukatar jam'iyyarsu ta lashe zaben shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Yadda Wani Gwamna da Ayu suka Kitsawa Wike Kullaliya inji Jang

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon gwamnan ya ce, zuwansa Ogun ba komai bane face ziyara da kai-da-kai, kuma bai yi wani karin haske kan abin da suka tattauna ba.

Kallon uba nake yiwa Obasanjo, inji Modu Sheriff

Ya kuma bayyana Obasanjo a matsayin uba a gareshi, inda yace yakan ziyarce shi ne a matsayin da.

A kamalansa:

"Baba tsohon dattijon kasa ne. Idan da Najeriya kamfani ne, to Baba shi ne shugabanta/shugaban gudanarwarta. Saboda haka nakan zo yin shawari da ubana kuma na yi tattaunawar kai-da-kai dashi.
"Nine karamin ciki. Lokaci zuwa lokaci, dole na zo gaida mahaifina, mu tattauna a sirrance sannan na tafi."

Sheriff, wanda kuma jigo ne a jam'iyyar APC ya ce ziyartar Obasanjo a wurinsa ya zama jiki, domin yakan zo a lokuta da dama.

Meye alakar ganawarsa da Obansajo da zaben 2023?

Kara karanta wannan

Tinubu Babban Kadarane, Gwamna Ganduje Ya Bayyana Kadan Daga Halayen Tinubu

Yayin da aka tambaye shi ko ganawar tasu na da alaka da batun Najeriya, ya ce sam ba haka bane, rahoton Daily Post.

Game da zaben 2023 kuwa, jigon na APC ya ce, yana da burin ganin APC ta ci gaba da mulki daga inda Buhari ya tsaya.

Bai dai yi karin haske gama da makomar siyasarsa ba, bai kuma yi magana kan wanda za a zaba a zaben 2023 ba.

Ali Modu Sheriff dai tsohon shugaban jam'iyyar adawa ta PDP ne, a yanzu kuma ya zama babban jigo a jam'iyya mai ci ta APC.

Ina da Dangantaka Mai Karfi da Sarauniyar Ingila Elizabeth II, Tsohon Shugaban Najeriya Obasanjo

A wani labarin, a yayin da ake ci gaba da jigilar binne sarauniyar Ingila Elizabeth II, tsohon shugaban kasa a Najeriya, Olusegun Obasanjo ya yi wata magana mai daukar hankali.

Obansaji ya ce yana alaka da dangantaka mai karfi da sarauniya Elizabeth II, inda yace yana mata fatan alheri kuma yana matukar girmama ta, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Komai Ya Dagule, Nan Ba da Jimawa Ba Zamu Haɗa Kan Atiku da Wike, Shugaban BoT-PDP

A wata sanarwa da Obasanjo ya fitar ta hannun hadiminsa, Kehinde Akinyemi, ya ce sarauniya na da halin dattaku da iya zama da mutane, kuma shi kansa yana kyakkyawar dangantaka ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel