Ina da Dangantaka Mai Karfi da Sarauniyar Ingila Elizabeth II, Tsohon Shugaban Najeriya Obasanjo

Ina da Dangantaka Mai Karfi da Sarauniyar Ingila Elizabeth II, Tsohon Shugaban Najeriya Obasanjo

  • Tsohon shugaban kasan Najeriya, Obasanjo ya bayyana alakarsa da marigayiyi sarauniyar Ingila
  • Obasanjo ya ce yana matukar mutunta sarauniya Elizabeth II, kuma tabbas ya taba ganawa da ita
  • A yau ne ake jigilar jana'izar karshe ta sarauniya Elizabeth II, shugabannin duniya sun halarci taron

Najeriya - A yayin da ake ci gaba da jigilar binne sarauniyar Ingila Elizabeth II, tsohon shugaban kasa a Najeriya, Olusegun Obasanjo ya yi wata magana mai daukar hankali.

Obansaji ya ce yana alaka da dangantaka mai karfi da sarauniya Elizabeth II, inda yace yana mata fatan alheri kuma yana matukar girmama ta, Daily Trust ta ruwaito.

Obasanjo ya fadi alakarsa da sarauniyar Ingila
Ina da Dangantaka Mai Karfi da Sarauniyar Ingila Elizabeth II, Tsohon Shugaban Najeriya Obasanjo | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A wata sanarwa da Obasanjo ya fitar ta hannun hadiminsa, Kehinde Akinyemi, ya ce sarauniya na da halin dattaku da iya zama da mutane, kuma shi kansa yana kyakkyawar dangantaka ita.

Hakzalika, ya kuma mika ta'aziyya da jimaminsa ga wannan babban rashi da duniya ta shaida a 2022 na mutuwar sarauniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda na gana da sarauniya - Obasanjo

Ya kuma bayyana kadan daga tarihi, inda yace yana dab da kammala karatun sakandare a lokacin da sarauniyar ta taba kawo ziyarar Najeriya

A bangare guda, ya ce ya yi farin cikin ganawa da sarauniyar tare da tarbarta a 2003 taron Shugabannin Kasashe Renon Ingila na CHOGM a Abuja.

Jaridar Premium Times ta ruwaito shi yana cewa:

"Alaka ta da sarauniya kyakkyawa ce, tana da matukar girma, mace mai girma, wacce ta zama misali mai tasiri a hulda da jama'a. Ta dauki kanta da girma, da mutunci. Ita mace ce da nake matukar mutuntawa."

Daga karshe, ya mika ta'aziyyarsa ga sabon sarkin Ingila, Charles da ma sauran jama'a a duniya da suka dandana rashin sarauniya.

Rayuwata Na Cikin Hadari Tun Bayan Yiwa Sarauniyar Ingila Elizabeth II Mummunan Fata, Farfesa Uju Anya

A wani labarin, Farfesa 'yar Najeriyar nan dake zaune a Amurka da ta yi fatan mutuwa mai radadi ga sarauniyar Ingila ta bayyana cewa, rayuwarta na cikin matsanancin hali.

Uju Anya farfesa ce a sashen Harsunan Zamani a Jami’ar Carnegie Mellon ta kasar Amurka, in ji jaridar The Punch.

Farfesar ta jawo cece-kuce a kafar sada zumunta ta Twitter a ranar da aka sanar da cewa sarauniyar Ingila na can kwance jina-jina a asibiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel