Zamu Hada Kan Atiku da Gwamna Wike Nan Ba Da Jimawa Ba, Shugaban BoT-PDP

Zamu Hada Kan Atiku da Gwamna Wike Nan Ba Da Jimawa Ba, Shugaban BoT-PDP

  • Shugaban BoT na jam'iyyar PDP ta ƙasa, Sanata Wabara, ya kai ziyarar neman sulhu ga gwamna jihar Benuwai, Samuel Ortom
  • Tsohon shugaban majalisar dattawa yace komai ya dagule a PDP amma nan ba da jimawa ba zasu shawo kan komai
  • Gwamna Ortom yace ra'ayinsa ɗaya da abokinsa gwamna Wike amma BoT ta fara abinda ya kamata

Benue - Tsohon shugaban majalisar dattawa kuma shugaban kwamitin amintattu (BoT) na PDP ta ƙasa, Sanata Adolphus Wabara, yace nan ba da jimawa ba za'a warware rikicin da ya addabi jam'iyyar.

Wabara ya ba da wannan tabbacin ne ranar Laraba a Makurdi yayin da ya jagoranci Mambobin BoT suka kai ziyarar neman sulhu ga gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai.

Sanata Adolphus Wabara.
Zamu Hada Kan Atiku da Gwamna Wike Nan Ba Da Jimawa Ba, Shugaban BoT-PDP Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta ruwaito Sanata Wabara na kuranta gwamna Ortom da cewa mutum ne mai babban murya kuma jigo abin misali a jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Shugaban Jam’iyyar Kwankwaso Yace Likimo Tinubu Zai Dunga Yi A Bakin Aiki Idan Ya Zama Shugaban Kasa

Da yake zantawa da yan jarida bayan kaddamar da wani aiki a cikin gidan gwamnatin Benuwai, tsohon shugaban majalisar dattawan ya amince da batun cewa ba abinda ke tafiya dai-dai a PDP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa yace:

"Babu iyalan da ba su da matsala kuma wannan ne makasudin zuwan mu nan domin mu samu kwarin guiwa tare da shawarawari. Kamar yadda na faɗa tun farko babu matsalar da bata da hanyar warware wa."
"Ya kamata mu san abinda bakunan mu zasu furta domin wataran zamu wayi gari a kan teburi ɗaya saboda yan Najeriya. Mun zo nan ne saboda samun damar isa ga mambobin da suka fusata."
"Suna da dalili mai ƙarfi, zamu yi nazari a jam'iyya mu yanke hukunci nan ba da jima wa ba. Kowa ya san cewa PDP ce kaɗai zata iya, Allah ya umarci mu kauce na shekara 8 ne saboda yan Najeriya su wa kansu alƙalanci."

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa A 2023: Tinubu Na Da Karfin Da Zai Iya Farfado Da Najeriya, Yahaya Bello

Mun jima tare da Wike inji Ortom

Da yake jawabi, gwamna Ortom ya yaba wa tawagar bisa ɗaura neman hanyar sulhu, inda a cewarsa tun farko ya kamata a yi haka.

Gwamnan wanda ya sa kanshi a cikin mambobin da suka fusata, yace, "Na jima tare da Wike, mu abokan juna ne kuma abokan aiki, kuma ra'ayin mu ɗaya kan wannan batun."

A wani labarin kuma Bayan Su Wike, Wasu Kusoshin Siyasa a Tafiyar Atiku Sun Goyi Bayan Tinubu a 2023

Jam'iyyar PDM, wacce marigayi Shehu Musa Yar'adua ya kafa daga baya ta koma tafiyar siyasar Atiku, ta yi watsi da tsohon mataimakin shugaban.

Jam'iyyar wacce aka rushe ta ayyana goyon bayanta ga Tinubu na APC tare da wasu ƙungiyoyi, sun ce shi ya fi dacewa da shugabanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel