Tinubu Babban Kadarane, Gwamna Ganduje Ya Bayyana Kadan Daga Halayen Tinubu

Tinubu Babban Kadarane, Gwamna Ganduje Ya Bayyana Kadan Daga Halayen Tinubu

  • Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya sha alwashin yin aiki tukuru don ganin Bola Tinubu ya dare kujerar Shugaba Buhari a 2023
  • Ganduje ya ce Tinubu mutum ne mai mutunci kuma babban kadara wanda zai kawo ci gaba a kasar idan har ya zama shugaban kasa
  • Ya ce tsohon gwamnan na jihar Lagas ya taka rawargani wajen kawo mulkin damokradiyya wanda yan Najeriya ke morewa a yanzu

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa idan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya lashe zabe zai bunkasa kasar tare da kawo ci gaba.

Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin da yake karbar nadin da aka yi masa a matsayin uban kungiyar ANIM a gidan gwamnati da ke Kano, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Jigon APC Ya Bayyana Adadin Kuri'un Da Tinubu Zai Samu Daga Yankin Yarbawa

Ganduje da Tinubu
Tinubu Babban Kadarane, Gwamna Ganduje Ya Bayyana Kadan Daga Halayen Tinubu Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Gwamnan ya ce:

“Tarihin da Tinubu ya kafa ya nuna cewa zai iya ciyar da Najeriya gaba idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Asiwaju mutum ne mai mutunci kuma babban kadarane. Ya bayar da gudunmawa sosai a wajen ci gaban damokradiyyarmu.
“Ya kasance cikakken dan damokradiyya kuma jagora mai nasara wanda ya sha gwagwarmaya don kawo mulkin damokradiyya da yan Najeriya ke morewa a yau.”

Ya bukaci kungiyar ANIM da su hada kai da kuma baiwa Tinubu cikakken goyon bayansu bayan zaben shugaban kasa na 2023.

Ganduje ya nuna goyon godiyarsa a kan karramawar da kungiyar tayi masa sannan ya yi alkawarin aiki tukuru don ganin nasarar Asiwaju a matsayin shugaban kasa, rahoton Daily Post.

Da farko, shugaban ANIM, Alhaji Sadik Fakai, ya bayyana cewa nadin wata hanya ce ta nuna godiya ga rawar ganin da Ganduje ya taka wajen tabbatar da Asiwaju a matsayin dan takarar APC.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan PDP Mai Karfin Fada A Ji Ya Bayyana Matsayin Jam'iyyar Janyewar Wike Da Mutanensa Daga Takarar Atiku

Shugaban Jam’iyyar Kwankwaso Yace Likimo Tinubu Zai Dunga Yi A Bakin Aiki Idan Ya Zama Shugaban Kasa

A wani labarin, shugaban jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP), Rufai Ahmed Alkali, ya bayyana dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, a matsayin wanda zai zama ‘shugaban kasa mai likimo’.

Ahmed Alkali ya bukaci yan Najeriya da su tabbata basu zabi tsohon gwamnan na jihar Lagas ba.

Dan yake martani ga wani hoton Tinubu da ya yadu inda aka gano shi yana bacci a fadar sarkin Gombe a karshen mako, Alkali ya ce NNPP na aiki tukuru domin lashen zaben shugaban kasa na 2023, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel