Rigimar Takara: An Kai Shugaban Jam’iyyar PDP da Jagororin Jam’iyya Gaban IGP

Rigimar Takara: An Kai Shugaban Jam’iyyar PDP da Jagororin Jam’iyya Gaban IGP

  • Ana rikici a kan takarar kujerar Sanata tsakanin Jibrin Tatabe da Hon. Mohammed Umara Kumalia
  • Hon. Jibrin Tatabe yace shi ya lashe zaben tsaida gwani, amma aka ba Mohammed Kumalia tikitinsa
  • A dalilin haka ‘Dan siyasar ya gabatar da korafi a kan shugaban jam’iyyar PDP ga Shugaban ‘Yan Sanda na kasa

Abuja - Jibrin Tatabe ya kalubalanci shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu a dalilin hana shi takarar Sanata da yace an yi ba tare da dalili ba.

Daily Trust ta ce Honarabul Jibrin Tatabe ya yi karar Dr. Iyorchia Ayu da shugabannin jam’iyyar PDP ga Sufeta Janar na ‘yan sandan kasa.

Jibrin Tatabe ya gabatar da korafin da ya nuna an zalunce sa a wajen hana shi takarar kujerar majalisar dattawa na shiyyar Borno ta tsakiya.

Kara karanta wannan

Shugaban Jam’iyyar Kwankwaso Yace Likimo Tinubu Zai Dunga Yi A Bakin Aiki Idan Ya Zama Shugaban Kasa

Shu’aibu Mu’azu da wasu Lauyoyi suka sa hannu a korafin da aka fitar a ranar 4 ga watan Agusta. Tatabe yace bai taba janye takarar da yake yi ba.

Korafin Jibrin Tatabe

“Nayi rubutu domin nuna damuwa a kan karfa-karfa da zalunci da jam’iyyar PDP ta yi mani.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tun bayan zaben shugabanninmu da zaben fitar da gwani inda aka tsaida ‘yan takara, wadanda ke rike da jam’iyyarmu suke yi mani karfa-karfa.
Jibrin Tatabe
Hon. Jibrin Tatabe Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC
Nayi takara kuma na lashe zaben fitar da gwani da aka yi a garin Maiduguri a ranar 23 ga watan Mayu 2022, na doke abokin takarata da kuri’u 244.
Jam’iyya ta ba ni takardar shaidar nasara, sai wasu ‘yan siyasan Borno da suka tare a Abuja, wanda ba su taimakon al’umma, suka yi ta neman canza ni.
An nemi a maye gurbina da Hon. Mohammed Umara Kumalia wanda bai ci zaben tsaida gwani ba, sun san ba zai ci zabe ba, sai na ki amincewa.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Gwamnoni, tsaffin ministoci, jiga-jigai masu goyon bayan Wike sun yi hannun riga da kwamitin kamfen PDP

- Jibrin Tatabe

Kumalia ba 'Dan APC ba ne

Tatabe ta bakin Lauyoyinsa ya shaidawa IGP cewa wanda aka maye gurbinsa da shi ba cikakken ‘dan jam’iyyar hamayyar ba ne, daga APC ya fito.

Premium Times tace Tatabe yana neman a karbe takarar daga hannun Mohammed Kumalia, a cewarsa ya kai kara wajen jam'iyya, ba ayi komai ba.

PDM za ta bi APC

Mun samu labari Jam’iyyar Peoples Democratic Movement (PDM) da INEC ta soke rajistarta, za ta bi APC a zaben 2023, maimakon Atiku Abubakar.

Shugabannin PDM sun ce sun fahimci Bola Tinubu ne ya fi dacewa da ya jagoranci ragamar gwamnati duk da cewa Atiku yana da alaka da jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel