Jiga-jigan PDP masu goyon bayan Wike sun fita daga kwamitin kamfen PDP

Jiga-jigan PDP masu goyon bayan Wike sun fita daga kwamitin kamfen PDP

  • Rikicin jam'iyyar adawa ta PDP ta dau sabon salo yayinda manyan jiga-jiganta sukayi hannun riga da yakin neman zaben Atiku
  • Gwamnoni, tsaffin gwamnoni, iyayen jam'iyya sun ce sai an cire Iyorchia Ayu zasu taya Atiku Abbuakar yakin neman zabe
  • Atiku Abubakar ne dan takaran kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023

Rivers - Jiga-jigan jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) masu goyon bayan gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, sun yi hannun riga da yakin neman zaben Atiku Abubakar, dan takarar kujerar shugaban kasa.

Sanarwa ta fito da sanyin safiyar Laraba a karshen zaman da sukayi a gidan Wike dake karamar hukumar Obio-Akpor ta jihar Rivers, rahoton TheNation.

Sun lashi takobin cewa lallai fa sai shugaban uwar jam’iyyar PDP Iyorchia Ayu ya yi murabus.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC Ba Ta Dan Takaran Gwamna a Zaben 2023, Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin Bwacha

THISDAY ta ruwaito cewa wadanda suka halarci zaman sun hada da wasu gwamnoni, tsaffin gwamnoni, tsaffin ministoci, jiga-jigan jam'iyya, har da iyayaen jam'iyyar.

Wikee
Jiga-jigan PDP masu goyon bayan Wike sun fita daga kwamitin kamfen PDP Hoto: Arise News
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar, Olabodoe George, a karshen zaman ya yi jawabi ga manema labarai.

Yayin karanto jawabin shawarar da suka yanke, Olabode George yace sun damu matuka game da barakar dake cikin jam'iyyar.

Ya ce ko shakka babu ba zasu yarda da Iyorchia Ayu ba kuma cigaba da kasancewa shugaban jam'iyyar ya sabawa kundin tsarin mulkin PDP.

Sun tuhumci Ayu da kulla makarkashiya a zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa da akayi ranar 28 da 29 ga Mayu.

A cewarsa:

"Mun damu matuka da rabuwar kan dake cikin jam'iyyarmu. Wallafa takardar kwamitin kamfe ba tare da dinke barakar ba rashin azanci ne."
"Wajibi ne Sanata Iyorchia Ayu yayi murabus a matsayin shugaban uwar jam'iyya kuma a nada sabon shugaba daga yankin kudu kuma shugaban kamfe daga yankin kudu."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotu Ta Zabi Ranar Gardama Tsakanin Gwamnati Da ASUU

"Saboda haka mun yanke shawarar ba zamu sa hannu cikin kamfe ba har sai Dr Iyorchia Ayu ya yi murabus."

Asali: Legit.ng

Online view pixel