Shugaban Jam’iyyar Kwankwaso Yace Likimo Tinubu Zai Dunga Yi A Bakin Aiki Idan Ya Zama Shugaban Kasa

Shugaban Jam’iyyar Kwankwaso Yace Likimo Tinubu Zai Dunga Yi A Bakin Aiki Idan Ya Zama Shugaban Kasa

  • Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Rufai Ahmed Alkali, ya yi gargadi cewa dan takarar APC, Bola Tinubu zai zama ‘shugaban kasa mai likimo’ idan aka zabe shi a 2023
  • Alkali ya gargadi masu kada kuri’u da su tabbatar da ganin cewa basu zabi tsohon gwamnan na jihar Lagas ba
  • A cewarsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar kayan marmari shine yafi dacewa da kowani dan Najeriya

Abuja - Shugaban jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP), Rufai Ahmed Alkali, ya bayyana dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, a matsayin wanda zai zama ‘shugaban kasa mai likimo’.

Ahmed Alkali ya bukaci yan Najeriya da su tabbata basu zabi tsohon gwamnan na jihar Lagas ba.

Dan yake martani ga wani hoton Tinubu da ya yadu inda aka gano shi yana bacci a fadar sarkin Gombe a karshen mako, Alkali ya ce NNPP na aiki tukuru domin lashen zaben shugaban kasa na 2023, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Jiga-jigan APC da Tinubu
Shugaban Jam’iyyar Kwankwaso Yace Likimo Tinubu Zai Dunga Yi A Bakin Aiki Idan Ya Zama Shugaban Kasa Hoto: @ayemojubar
Asali: Twitter

Ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata, 20 ga watan Satumba, yayin horar da sakatarori da hadiman yan takarar shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa na NNPP a wani atisaye na kwana biyu kan soshiyal midiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce abun mamaki ne cewa dan takarar shugaban kasar ya fara likimo a wajen taro tun kafin a fara kamfen gabannin zaben na 2023.

Jaridar ta nakalto Alkali yana cewa:

“Ta yaya dan takarar shugaban kasa zai fara bacci tunma kafin a fara kamfen? Wato hakan na nufin idan kuka zabe shi, za ku kasance da shugaban kasa mai likimo na tsawon shekaru hudu masu zuwa. Abun da kuke so kenan – shugaban kasa mai likimo? Kuna da kwarin gwiwa a kansa?”
“Dr Rabiu Musa Kwankwaso mutum ne mai kishi, mutum ne mai kwarin gwiwa, mutum ne jajirtacce kuma mutum ne wanda ya rigada ya yi abubuwa da dama a rayuwarsa.”

Gwamnan Arewa Ya Bayyana Wadanda Za Su Tafiyar Da Gwamnatin Tinubu Idan Aka Zabe Shi

A wani labarin, gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana cewa matasa ne za su tafiyar da gwamnatin Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) idan aka zabe shi.

Bello na daya daga cikin sabbin mambobin kungiyar kamfen din Tinubu-Shettima inda aka nada shi a matsayin jagoran matasanta na kasa, Vanguard ta rahoto.

Yayin da yake sanar da nadin nasa, Tinubu ya bayyana nasarorin siyasa da irin shugabanci abun koyi da gwamnan ya nuna a jiharsa da kuma a matsayinsa na dan jam’iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel