Tsohuwar Jam’iyyar Atiku Ta Juya Masa Baya, Za Tayi Wa Tinubu Aiki a Zaben 2023

Tsohuwar Jam’iyyar Atiku Ta Juya Masa Baya, Za Tayi Wa Tinubu Aiki a Zaben 2023

  • Jam’iyyar Peoples Democratic Movement (PDM) da INEC ta soke rajistarta, za ta bi APC a zaben 2023
  • Shugabannin PDM sun ce sun fahimci Bola Tinubu ne ya fi dacewa da ya jagoranci ragamar gwamnati
  • PDM tana tare da ‘Yan Muslim/Christian Youths & Elders Forum da Genuine Governance Group

Abuja - ‘Yan tsohuwar jam’iyyar Democratic Movement wanda tuni ta ruguje, suna cikin wadanda ke goyon bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a 2023.

A rahoton da This Day ta fitar a makon nan, an ji cewa Bola Tinubu yana tare da ‘yan tafiyar PDM da kungiyar GGG ta dattawan Musulmai da Kiristoci.

Marigayi Manjo Janar Shehu Musa Yar’Adua mai ritaya ya kafa tafiyar PDM wanda aka yi wa rajista a matsayin jam’iyyar siyasa can bayan ya rasu.

Kara karanta wannan

Bayan Su Wike, Wasu Kusoshin Siyasa a Tafiyar Atiku Sun Koma Bayan Tinubu a Zaɓen 2023

Atiku Abubakar yana cikin manyan yaran Shehu Yar’Adua a siyasa, kuma yana tare da PDM ne aka dauko shi ya zama mataimakin shugaban Najeriya.

A yanzu da hukumar INEC ta soke rajistar PDM, jam’iyyar ta wagaje, anyi tunanin ‘ya ‘yanta za su goyi bayan Atiku ya karbi shugabanci a zabe mai zuwa.

Tinubu ya fi cancanta a 2023 - PDM

Shugaban tafiyar a Najeriya, Cif Frank Igwebuike da sakatariyarsa, Maimunat Ahmadu sun shaidawa manema labarai PDM na nan da ofisoshinta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu
Asiwaju Bola Tinubu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Jagororin jam’iyyar suka ce suna da ofis a Abuja da jihohi 36, kuma bayan dogon nazarin ‘yan takara, sun fahimci Bola Tinubu ya fi kowa cancanta.

Bayan tashinmu daga taron NEC, mun amince za muyi aiki domin Asiwaju Bola Tinubu ya samu nasarar lashe kujerar shugaban kasar tarayyar Najeriya a 2023

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sanata Shekarau Ya Sanar da Matakin Sauya Sheka a Zaman Majalisar Dattawa

- Frank Igwebuike

Shigowar Triple GEE

The Nation ta rahoto Igwebuikeyan yana cewa kungiyar Genuine Governance Group wanda aka fi sani da GGG tana tare da ita a kan wannan zabi da tayi.

GGG kungiya ce ta tsofaffin ‘yan majalisa, kungiyoyi masu zaman kansu, da masu fada a ji, wanda ta shirya goyon bayan ‘dan takaran da ya cancanci mulki.

A cewar Igwebuike, akwai Musulmai da Kiristoci masu kishin kasa da ke cikin tafiyarsu, wadanda za su yaki takarar Atiku Abubakar a zaben 2023.

Lawan a 2023

‘Yan takara 4,223 za suyi takarar kujerun Majalisar tarayya, inda aka ji labari a Yobe babu sunan Ahmad Lawan wanda shi ne Shugaban majalisa a yanzu.

Tun bayan zaben 1999, Ahmad Lawan ya tare a Majalisa Wakian tarayya, daga baya ya zama Sanata, sai a 2023 ake neman kawo masa barazana a siyasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel