Tsohon Hadimin Buhari Ya Shigo Takarar Gwamnan Kano Gadan-Gadan Daga Baya

Tsohon Hadimin Buhari Ya Shigo Takarar Gwamnan Kano Gadan-Gadan Daga Baya

  • Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada zai yi takarar Gwamna a karkashin jam’iyyar adawa ta ADP mai alamar littafi
  • ‘Dan majalisar na Birnin Kano ya fice daga APC bayan dogon lokacin ana samun sabani, ya samu takara a ADP
  • Sha’aban Ibrahim Sharada zai gwabza da Nasiru Gawuna, Abba Kabir Yusuf, Sadiq Wali da wasu ‘yan takara a 2023

Kano - Tsohon Mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara, Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada ya fito takarar gwamna a jam’iyyar ADP.

Rahoton Daily Trust yace Honarabul Sha’aban Ibrahim Sharada ya shaidawa mutanen Kano burinsa da ya ayyana niyyar neman Gwamna

An yi wani taro a cibiyar matasa ta Sani Abacha Youth a Kano a ranar Lahadi, 4 ga watan Satumba 2022, inda ‘dan takaran ya nuna ga gaske yake yi.

Legit.ng Hausa ta fahimci mutane da-dama a Kano sun samu halartar taron da Sharada ya kira.

Kara karanta wannan

APC ta Dakatar da Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisa Saboda Ya Hada-kai da PDP

Dauda Kahutu Rarara yayi wasa a wajen taron, ya kuma gabatar da wasu ‘yan takarar ADP irinsu Aminu Ladan Abubukar da Adam Abdullahi Adam.

Tirka-tirka a jam’iyyar ADP

Legit.ng Hausa ta fahimci wannan na zuwa ne a lokacin da Nasiru Koguna yake ikirarin shi ne asalin ‘dan takaran ADP a zaben Kano ba Sharada ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A zaben fitar da gwani da aka yi a watan Yuni, Koguna aka sanar a matsayin ‘dan takaran jam’iyyar ADP, amma sai daga baya ne maganar ta canza.

Sha’aban Sharada
Takarar Sha’aban Sharada Hoto: @Ameenu_Kutama
Asali: Twitter

Shugabannin jam’iyyar ta ADP mai alamar littafi sun ce Hon. Sharada ne ‘dan takara a 2023.

Siyasar Kano a 2023

Hon. Sharada zai nemi takarar gwamnan jihar Kano ne a karkashin jam’iyyar hamayya ta Action Democratic Party (ADP), bayan ya fice daga APC.

A halin yanzu jam’iyyar APC ta tsaida Nasiru Yusuf Gawuna da Murtala Sule Garo, mataimakan gwamna mai-ci da tsohon kwamishina a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Dalilan da suka Jawo Tinubu da Gwamnoni 5 Suka Ziyarci Jonathan Sun Farawa Fitowa

An ji labari PDP ta ba Sadiq Wali da Yusuf Bello Dambatta takara, dukkaninsu sun rike kwamishononi a gwamnatin Ganduje da kuma na Kwankwaso.

Ku na da labari jam’iyyar NNPP kuwa ta tsaida Abba Kabir Yusuf da Aminu Abdussalam Gwarzo ne, wadanda suka yi takara a PDP a zaben 2019.

Tsohon kwamishina kuma jigo a APC, Bala Gwagwarwa shi ne wanda zai yi takarar gwamna a SDP, yayin da Salihu Tanko Yakasai yake yin takara a PRP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel