Kano 2023: INEC ta yi watsi da dan Abacha, ta zabi Wali ya yi takarar gwamna a PDP

Kano 2023: INEC ta yi watsi da dan Abacha, ta zabi Wali ya yi takarar gwamna a PDP

  • Jam'iyyar PDP a jihar Kano ta samu dan takarar gwamna, INEC ta fitar sunayen masu takarar gwamna a jihohin Najeriya
  • An samu hargitsi a PDP ta jihar Kano yayin da aka gudanar zaben fidda gwanin dan takarar gwamna a 203
  • An samu jihohin da aka samu rikicin cikin gida a jam'iyyu daban-daban na siyasa, lamarin da ke kawo rarrabuwar kai

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ayyana suna tare da tantance Sadik Wali a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kano.

Hakan ya haifar da rudani a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar da ke tsagin zartaswar jihar karkashin jagorancin Shehu Sagagi.

Daily Trust ta ruwaito cewa rikicin da ya barke a jam’iyyar ta Kano ya kai ga gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar a tsagi biyu.

INEC ta zabi wani, ta yi waje da dan Abacha
Kano 2023: INEC ta yi watsi da dan Abacha, ta zabi Wali ya yi takarar gwamna a PDP | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Hakan dai ya haifar da samun ‘yan takarar shugaban kasa mabambanta a jam'iyyar ta PDP mai adawa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwamishinan zabe na jihar, Farfesa Riskuwa Shehu, ya shaida wa manema labarai a ranar 30 ga watan Yuni cewa hukumar ta sanya ido kan zaben fidda gwanin da Shehu Wada Sagagi ke jagoranta wanda ya samar da Abacha a matsayin dan takarar gwamna.

Amma sunayen da aka lika na 'yan takarar gwamna a ranar Juma’a a ofisoshin INEC na jihar, an gano, cewa an bayyana sunan Wali da na mataimakinsa Yusuf Dambatta a bangon ofishin INEC na Kano.

Da yake mayar da martani kan lamarin, jami’in hulda da jama’a na INEC na jihar Kano, Ahmad Adam Maulud, ya ce hukumar a matakin jiha ta mika abin da sakamakon zaben fidda gwanin ya samar ga hedikwatar ta kasa.

Ya ce abin da aka manna a bangon INEC ranar Juma’a shi ne abin da aka ya dawo daga hedikwatar INEC ta kasar.

A cewar jami'in:

"Mun tura abin da muka yi zuwa hedkwatarmu ta kasa kuma abin da muka manna a yau (Juma'a) ya fito ne daga gare su kai tsaye."
"Duk wanda ke son neman karin haske ya tuntubi cibiyar jam'iyyarsa ta kasa don samun bayanai."

Ta tabbata: INEC ta amince da takarar gwamnan Kano ga dan janar Abacha a PDP

A baya kunji cewa, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta tabbatar da cewa ta sa idon basira a zaben fidda gwani da ya samar da Mohammad Abacha a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kano.

Kafin bayanin na INEC dai an yi ta cece-kuce kan wanda hukumar za ta amince da shi a matsayin dan takarar gwamna tsakanin Mohammed Abacha da Sadiq Wali.

Kwamishinan zabe na yanki (REC), Farfesa Riskuwa Shehu, ya tabbatar wa manema labarai hakan a Kano, a ranar Alhamis, 30 ga watan Yuni, in ji jaridar The Guardian.

Asali: Legit.ng

Online view pixel