Mataimakin Gwamnan Kano, Nasir Gawuna, ya lashe zaben fidda gwanin APC

Mataimakin Gwamnan Kano, Nasir Gawuna, ya lashe zaben fidda gwanin APC

  • Zabin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, watau Nasir Gawuna ya lashe zaben fidda gwanin jihar Kano
  • Gawuna wanda tuni daukacin mambobin jam'iyyar suka alanta matsayin wanda akayi ittifaki kansa ya doke Sha'aban Sharada
  • Sharada ya zargi gwamnatin da hana wasu deliget zabe inda za su bar wasu su yi sannan su yi amfani da sakamakon saboda Gawuna yayi nasara

Kano - Mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasir Gawuna, a ranar Juma'a ya lashe zaben fidda gwanin yan takaran gwamnan jihar Kano karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Gawuna, ya samu kuri'u 2,289, inda ya lallasa Sha'aban Sharada, wanda ya samu kuri'u 30.

Shugaban kwamitin zaben, Tijjani Yahaya, ya alanta Gawuna matsayin wanda yayi nasara a zaben.

A cewarsa:

"I Sen.Tijjani Yahaya Kaura, Shugaban zaben fidda gwanin gwamnan jihar Kano a madadin uwar jam'iyyarmu na sanar da sakamakon wannan zabe da aka kammala kuma na alanta Dr Nasiru Yusuf Gawuna wanda ya samu kuri'u mai rinjaye matsayin zakara."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Dr Dikko Radda ya lashe zaben fidda gwanin APC a jihar shugaban ƙasa

"Saboda haka shi ne zai daga tutar APC a zaben gwamnan jihar Kano da za'a yi a 2023."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mataimakin Gwamnan Kano, Nasir Gawuna, ya lashe zaben fidda gwanin APC
Mataimakin Gwamnan Kano, Nasir Gawuna, ya lashe zaben fidda gwanin APC Hoto: Aminu SSA Photography
Asali: Facebook

Sha'aban Sharada na zargin ana shirin tafka magudi a zaben fidda gwani saboda Gawuna

Gabanin sanar da sakamakon, Sha'aban Sharada, ya koka ka shirin da gwamnatin jihar ke yi na tafka magudin zaben fidda gwani saboda mataimakin gwamna Nasiru Gawuna.

Wannan korafin na dauke ne a wata takarda da aka sanya hannu a ranar Alhamis kuma aka aike ta zuwa shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ta hannun hukumar INEC ta Kano.

An aika kwafin wasikar ga shugaban jam'iyyar APC na kasa, sifeta janar na 'yan sanda, kwamishinan 'yan sandan jihar Kano da kuma hukumar tsaro ta farararn kaya ta jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel