Hadimin Ganduje da ya rasa kujerarsa kan sukar Buhari ya samu takarar Gwamnan Kano

Hadimin Ganduje da ya rasa kujerarsa kan sukar Buhari ya samu takarar Gwamnan Kano

  • Jam’iyyar PRP ta tsaida ‘dan takarar gwamnan jihar Kano a zaben da za a gudanar a shekarar 2023
  • Salihu Tanko Yakasai ne wanda ya yi nasarar lashe zaben fitar da gwani, zai rike tutar PRP a jihar Kano
  • Yakasai yana cikin wadanda suka yi aiki da Gwamna Abdullahi Ganduje masu neman zama gwamna

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Tsohon hadimin gwamnan jihar Kano, Salihu Tanko Yakasai wanda mutane suka sani da 'Dawisu', ya samu nasara a zaben jam’iyyar PRP.

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa Salihu Tanko Yakasai shi ne zai zama ‘dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar PRP a zaben 2023.

Malam Salihu Tanko Yakasai ya bada wannan sanarwa ne da kan shi a shafinsa na Twitter.

Da yake magana a ranar Lahadi, 5 ga watan Yuni, 2022, Yakasai ya nuna ya samu nasara a zaben da jam’iyyarsa ta shirya, zai rike mata tuta a Kano.

Kara karanta wannan

‘Yan takara na cikin rashin tabbas, PDP za tayi sabon zaben fitar da gwanin ‘Yan Majalisa

Salihu Tanko Yakasai ya godewa duk masu ruwa da tsaki na jam’iyyar hamayyar ta PRP da suka ba shi damar zama ‘dan takarar kujerar gwamna.

Sahara Reporters ta rahoto Dawisu yana cewa maganar yin takararsa a 2023 ta zama tabbas.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

'Dan takarar Gwamnan Kano
Salihu Tanko Yakasai Hoto: @Dawisu2016
Asali: UGC

"Alhamdulilah na lashe zaben fitar da gwanin jam’iyyata, yanzu kuma na zama ‘dan kujerar gwamnan jam’iyyar PRP mai alamar nasara a jihar Kano.”
“Ina matukar godiya ga masu zaben ‘dan takaran jam’iyyarmu, jagorori da masu fatan alheri. Yanzu batun #DawisunKano2023 ya tabbata.” - Salihu Yakasai.

Kafin ranar zaben, Yakasai ya ce wasu cikin masu neman kujerar gwamnan Kano a karkashin jam’iyyar ta PRP suka hakura da takarar, su ka ba shi wuri.

Salihu Yakasai wanda ya shiga siyasa shekaru 20 da suka wuce zai goge raini da Nasiru Yusuf Gawuna na APC da su Abba K. Yusuf a jam’iyyar NNPP.

Kara karanta wannan

Takarar Tinubu, Osinbajo, Amaechi da Lawan a 2023 ta na raba kawunan na-kusa da Buhari

Idan za a tuna, Yakasai ya rasa matsayinsa a gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ne bayan da ya soki gwamnatin Muhammadu Buhari a kan matsalar tsaro.

Bayan ya fito ya yi wasu maganganu, sai aka ji jami’an DSS sun cafke Mai ba gwamnan shawara. Makonni bayan an sallama shi daga aiki, sai ya fice daga APC.

Zaben APC na kasa

Dazu kun samu rahoto cewa jagororin siyasar Kudu maso yammacin Najeriya su na kokarin sasanta kan masu takarar shugabancin Najeriya a APC a 2023.

Sai dai wannan yunkuri bai haifar da ‘da mai ido ba, masu neman tikitin irinsu Bola Tinubu, Yemi Osinbajo da Gwamna Kayode Fayemu ba su da niyyar hakura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel