Ya Kamata Mu Sa Baki Domin Warware Matsalolin Najeriya, Osinbajo Ga Gwamnonin APC

Ya Kamata Mu Sa Baki Domin Warware Matsalolin Najeriya, Osinbajo Ga Gwamnonin APC

  • Yayin da yajin ASUU ke kara ta'azzara, mataimakin shugaban kasa ya yi alkawarin sa baki don kawo mafita
  • Hakazalika, ya ce lokaci ya yi da ya kamata a himmatu wajen magance dukkan matsalolin Najeriya
  • Kungiyar malaman jami'a ta shafe watanni tana yaji, ta ce ba za ta sake zama da jami'an gwamnatin Buhari ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Yayin da yajin aikin ASUU ya kara ta'azzara, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce to yanzu kam ya kamata na himmatuwa don warware matsalolin Najeriya baki daya.

An ruwaito Osinbajo na fadin haka ne a yau Talata 30 ga watan Agusta yayin da gwamnonin APC suka kai masa ziyarar sannu bayan murmurewarsa daga rashin lafiya, TheCable ta kawo.

Idan baku manta ba, an yiwa Osinbajo tiyata a gwiwarsa a kwanakin baya, lamarin da yasa ya tafi hutu.

Kara karanta wannan

ASUU Ta Sha Alwashin Kauracewa Sake Zaman Sasanci da Gwamnatin Tarayya

Osinbajo ya shiga batun ASUU, ya nemi hadin kan gwamnoni
Ya kamata mu sa baki domin warware matsalolin Najeriya, Osinbajo ga gwamnonin APC | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

A cewar batun da ya fito daga fadar gwamnati, shugabannin sun tattauna abubuwan da suka shafi yajin aikin ASUU da na tattalin arzikin Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta shafe kwanaki sama da 195 tana yajin aiki saboda wasu batutuwan da suka shafi jin dadin aiki da gwamnati ta gaza biya musu.

Malaman sun sha yin korafi kan rashin samun ababen more rayuwa a jami’o’in inda suka nemi gwamnati ta inganta harkar koyarwa a Najeriya.

Matakin gwamnati na gaba

Rahoton da muka samo ya ce, mataimakin shugaban kasa Osinbajo da da gwamnonin APC za su hada karfi da karfe wajen ganin an kawo mafita ga matsalolin da ke tattare da ASUU.

A cewar Osinbajo:

“Akwai bukatar dukkanmu mu hada kai tare kan wadannan muhimman batutuwa. Ya kamata mu yi tunanin mafita mai kyau, kuma akwai bukatar yin hakan cikin gaggawa.."

Kara karanta wannan

Yanzun nan: ASUU ta gama tattaunawa a Abuja, ta sake fitar da matsaya

Hakazalika, , ya kuma yaba da kokarin likitocin Najeriya wajen aiki tukuru da kuma tabbatar da iya amfani da kayayyakin magani a cibiyoyin lafiya a Najeriya.

Jerin wadanda suka halarci ganawar, inji rahoton This Day

  1. Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Dr Kayode Fayemi na jihar Ekiti
  2. Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato
  3. Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas
  4. Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa
  5. Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara
  6. Gwamna Abubakar Sani Bello na Jihar Neja
  7. Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun
  8. Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa
  9. Mataimakin gwamnan jihar Ebonyi, Kelechi Igwe

Jihohin Najeriya 10 Kacal Sun Fi Kasashen Afirka Girma, Inji Osinbajo

A wani labarin, farfesa Yemi Osinbajo, Mataimakin shugaban kasa a Najeriya, ya ce ba daidai bane ake kwatanta yanayin tattalin arzikin Najeriya da na sauran kananan kasashe a Afirka ba.

Osinbajo ya bayyana haka ne tare da cewa, akalla jihohi 10 na Najeriya kacal na da GDP din da ya girmi na wadancan kasashen na Afrika.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: ASUU ta shawarci Buhari kan yadda za a kawo karshen yajin aiki

Ya kuma shaida cewa, rahotannin marasa dadi da ke fitowa daga Najeriya ba su ke nuna gaskiyar yadda kasar baki daya take ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel