ASUU: Ba Zamu Sake Zama Da FG Ba Sai An Kafa Sabuwar Gwamnati

ASUU: Ba Zamu Sake Zama Da FG Ba Sai An Kafa Sabuwar Gwamnati

  • Alamu sun nuna cewa, Kungiyar ASUU ta ayyana yajin aikin sai Baba ta gani a fadin kasar nan bayan ganawar da suka yi
  • Wata majiya ta tabbatar da cewa, da yawan malaman sun bukaci shugabannin kungiyar su kauracewa zama da FG har sai an kafa sabuwar gwamnati
  • Wata majiya da NEC ta ASUU waccce ta bukaci a sakaya sunanta, tace ba zasu sake zama da gwamnatin Buhari ba

FCT, Abuja - Manyan alamu na nuna cewa, kungiyar malamai masu koyarwa na jami'o'in, ASUU, sun ayyana yajin aikin sai baba ta gani bayan gazawar gwamnatin tarayya na cika musu bukatunsu.

An gano cewa, malaman sun yanke wannan shawarar ne a yayin taron majalisar zartarwarsu wacce ta fara wurin karfe 12:15 na daren Litinin kuma ta dauka awanni a sakateriyar kungiyar dake jami'ar Abuja.

Takardar yadda aka kaya a taron wacce zata bayyana takamaiman hukuncin da suka yanke har yanzu basu saki ba, amma majiya mai karfi tace da yawan Malaman a fadin jami'o'in kasar nan sun goyi bayan tafiya yajin aikin sai baba ta gani.

An gano cewa, baya ga yajin aikin sai baba ta ganin, wasu Malaman sun shawarci kungiyar da ta kauracewa duk wani zama da zasu yi da gwamnatin tarayya har sai an kafa sabuwar gwamnati bayan tafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

ASUU ta ayyana yajin aikin da take ciki ne tun ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 kuma ya cigaba har tsawon wata shida a yanzu.

A yayin da Daily Trust ta ziyarci UniAbuja a ranar Lahadi, wani mamban ASUU yace taron ba wanda kafafen yada labarai bane zasu nada.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai wani mamban majalisar zartarwar ASUU wanda ya bukaci a sakaya sunansa, yace bayan ayyana yajin aikin sai baba ta gani, ba zasu sake zaman sasanci da gwamnatin tarayya ba.

A yayin da aka tambayesa mai hakan hake nufi, mamban NEC din ya ki cigaba da bayani.

Daliban Jami’a Sun Jefar da Shawarar Minista, Za Su Kai Gwamnati kotu kan ASUU

A wani labari na daban, kungiyar dalibai na kasar nan baki daya watau NANS, tace ta soma tattaunawa domin shigar da karar gwamnatin tarayya a kotu.

Punch ta ce a ranar Alhamis, 18 ga watan Agusta 2022, kungiyar ta NANS ta shaida mata cewa ta na kokarin yin shari’a da gwamnati da Ministan ilmi.

NANS tafitar da wani jawabi na musamman ga ‘yan jarida a garin Abuja, bayan Malam Adamu Adamu ya yi kira ga dalibai suyi karar malamansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel