Yajin Aiki: ASUU Ta Fadawa Buhari Abin da Ya Kamata Ya Koya Daga Mulkin Jonathan

Yajin Aiki: ASUU Ta Fadawa Buhari Abin da Ya Kamata Ya Koya Daga Mulkin Jonathan

  • Yayin da ASUU ta shafe kwanaki 195 tana yaji, shugaban kungiyar ya bayyana wata sabuwar mafita
  • Shugaban ya ce kamata yi Buhari ya yi duba ga tsohon shugaban kasa Jonathan domin koyi da mulkinsa
  • ASUU ta shiga yajin aiki a ranar 14 ga watan Fabrairun bana, dalibai da sauran 'yan Najeriya na cece-kuce a kai

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Shugaban kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), Emmanuel Osodeke ya shawarci gwamnatin Muhammadu Buhari da ta koyi darasi kan yadda za ta kawo karshen yajin aikin daga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Osodeke ya bayyana wannan shawari ne ga Buhari a wata hira da tashar AIT, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban ASUU ya ba Buhari shawarin kawo karshen yajin aiki
Yajin Aiki: ASUU Ta Fadawa Buhari Abin da Ya Kamata Ya Koya Daga Mulkin Jonathan | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A Emmanuel, gwamnatin Jonathan ta taba yin tattaunawar sa'o'i 14 da ASUU domin warware matsalolin da ASUU ke ciki.

Kara karanta wannan

Bacin rana: Wani ya yi aikin dana sani, ya kashe masoyiyarsa saboda katin ATM

Emmanuel ya dage cewa, kamata ya yi gwamnatin Buhari ta kafa kwamitin masoya Najeriya da za su kawo shawarwari masu kyau don ci gaban kasar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

“Ya kamata gwamnati ko sau daya ne ta koyi darasi daga Goodluck Jonathan. Wani lokaci cikin dare daya, mun yi tattaunawar sa'o'i 14. A fili. Bangarorin biyu kowa ya kasa kunne, babu jan aji, babu nuna iko, babu nuna ikon zama, kuma mun duba kowane batu kana muka warware komai cikin sa'o'i 14.
“Idan wannan gwamnatin za ta iya kafa wani kwamiti mai karfi, idan shugaban kasa ba zai hallara ba ma, to ya kokarta kawo mutanen da ba sa cikin wadanda a yanzu ke sharara karya a batun.
“Mutanen da ke kaunar kasar nan. Ba dole sai wadanda ke ci a gwamnati ba. Idan za ku iya hada komai yadda ya kamata wuri to za mu zauna mu ga yadda za magance wannan matsala ta kasa."

Kara karanta wannan

Da duminsa: Majalisar Zartaswar ASUU Zata Shiga Ganawa, Za’a Yanke Shawara Kan Lamarin Yajin Aiki

Ya zuwa yau Lahadi 28 ga watan Agusta, ASUU ta shafe kwanaki 195 tana yaji, wanda ta shiga tun ranar 14 ga watan Fabairun wannan shekarar, rahoton This Day.

Babu Abin da Malaman Jami’a Ke Tsinanawa a Jami’o’i, Don Haka Su Koma Aiki, Inji Farfesa Maqari

A wani labarin, Farfesa Ibrahim Maqari, limami a babban masallacin kasa da ke Abuja ya tona asirin malaman jami'a da irin kurarin da suke na binciken karya.

Farfesa Maqari ya ce, babu wani bincike da malaman jami'a ke yi, kawai suna shantakewa ne su koya wa dalibai abin da suke koyarwa sama da shekaru 20 da suka sani.

Wannan magana na Farfesa na zuwa ne daidai lokacin da malaman jami'a a Najeriya ke yajin aiki saboda rashin samun yadda suke so daga gwamnatin Najeriya na jin dadin aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel