Jihohin Najeriya 10 Kacal Sun Fi Kasashen Afirka Girma, Inji Osinbajo

Jihohin Najeriya 10 Kacal Sun Fi Kasashen Afirka Girma, Inji Osinbajo

  • Mataimakin shugaban kasa a Najeriya, Yemi Obasanjo ya bayyana kadan daga girman Najeriya
  • Osinbajo ya damu da yadda ake kwatanta tattalin arzikin Najeriya da sauran kasashen Afrika
  • Mutane da dama sun damu da yadda tattalin arzikin Najeriya ke kara tabarbarewa, musamman a mulkin Buhari

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Farfesa Yemi Osinbajo, Mataimakin shugaban kasa a Najeriya, ya ce ba daidai bane ake kwatanta yanayin tattalin arzikin Najeriya da na sauran kananan kasashe a Afirka ba.

Osinbajo ya bayyana haka ne tare da cewa, akalla jihohi 10 na Najeriya kacal na da GDP din da ya girmi na wadancan kasashen na Afrika.

Kasashen Afrika duka basu kai girman jihohin Najeriya 10 ba
Jihohin Najeriya goma sun fi kasashen Afirka girma – Osinbajo | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya kuma shaida cewa, rahotannin marasa dadi da ke fitowa daga Najeriya ba su ke nuna gaskiyar yadda kasar baki daya take ba.

Hakazalika, ya ce Najeriya kasa ce mai girman kasa, don haka ba ilahirin kasar ke fama da munanan abubuwan da ake gani a gidajen talabijin da gidajen jaridu ba.

Kara karanta wannan

Wata 6: Duk da aikin Hisbah, rahoto ya fadi kudin da 'yan Najeriya suka kashe a shan giya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce yana dai kyau kasashen duniya su fahimci irin yawan 'yan Najeriya da kuma girman fadin kasar domin su fahimci girman kalubalen da take fuskanta.

Hadiminsa kan harkokin yada labarai, Laolu Akande ya ce ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin daliban makarantar kasuwanci ta Harvard da suka ziyarce shi ranar Juma’a a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Daliban, waɗanda ke kan balaguron karin ilimi a Afirka, sun tattauna da Osinbajo kan fannonin jagoranci, addini, manufofin gwamnati, lafiya, tattalin arziki, da martabar kasa, da dai sauransu.

Misalin da Osinbajo ya bayar

Da yake rattaba misali da jihar Borno, ya ce ita kadai ta hade girman Burtaniya da Sweden ko Denmark, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

Ya ce:

“Misali, Borno kadai ta kai girman fadin Burtaniya hade da Sweden ko Denmark."

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: Sanusi da wasu sarakuna 9 da aka taba tsige su a kujerunsu a tarihin Najeriya

Hakazalika, ya ce Najeriya ba sa'ar sauran kasashen Afrika bane, don haka ya kamata a fahimci kasar da kyau.

Tattalin arziki: Mataimakin Shugaban kasa, Osinbajo ya yi wa Gwamnan CBN kaca-kaca

A wani labarin, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya soki tsarin da babban bankin Najeriya na CBN ya dauka a kan batun canjin kudin kasashen waje.

Premium Times tace Yemi Osinbajo ya ba babban bankin kasar shawara ya sake tunani kan batun canji.

Da yake magana a wajen taron bitar da aka shirya wa Ministoci a ranar Litinin, 11 ga watan Oktoba, 2021, Farfesa Osinbajo ya kawo wannan batun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel