Kada Ka Kuskura Ta Goyi Bayan Atiku, Mayaudari Ne, Inji Wani Jigon Siyasa

Kada Ka Kuskura Ta Goyi Bayan Atiku, Mayaudari Ne, Inji Wani Jigon Siyasa

  • Wani jigon siyasa ya shawarci gwamna Wike na jihar Ribas da ya marawa Bola Tinubu na APC ko Peter Obi na Jam’iyyar Labour baya a zaben 2023
  • Osita Okechukwu, wanda shi ne babban darakta na gidan rediyon VON ya fadi wannan ne sa'o;i kadan bayan ganawar Wike da Tinubu
  • Wasu hotuna sun nuna lokacin da gwamnan na jihar Ribas yake ganawa da jiga-jigan siyasar Najeriya

Najeriya - Babban daraktan gidan rediyon VON, Osita Okechukwu ya shawarci gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da kada ya kuskura ya mara wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar baya.

A 'yan kwanakin nan gwamna Wike na ganawa da jiga-jigan siyasar Najeriya a jam'iyyu mabambanta, lamarin da ke kara kada hantar Atiku.

A jiya Alhamis, 25 ga watan Agusta ne gwamnan ya gana da dan takarar shugaban na APC, Bola Tinubu da kuma Peter Obi na jam'iyyar Labour a birnin Landan.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan Ganawa Da Atiku A Birtaniya, Wike, Ortom Da Ikpeazu Sun Dira A Port Harcourt

Kada ka amince da goyon bayan Atiku, shawarin shugaban VON ga Wike
Kada ka kuskura ta goyi bayan Atiku, mayaudari ne, inji wani jigon siyasa | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Haka nan, ya gana da tsohon shugaban kasan Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo duk dai a birnin na Landan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kada ka bata siyasarka

Da yake tsokaci game da makomar siyasar Wike, Okechukwu ya gargadi gwamnan da kada ya bari ya kassara a harkokin siyasa a kasar nan, inji rahoton TheCable.

Ya ce a yanzu dai gwamnan na jihar Ribas na more yadda harkokinsa ke tafiya, don haka ne ma yake jan hankalin jiga-jigan siyasa da dama.

Shugaban na VON ya shawarci gwamna Wike da ya yi biris da batun Atiku bisa zargin yaudararsa (Wike) da ma yankin kudu.

A cewar Osita:

“Shawarata ita ce, kada ya kuskura ya sakawa Atiku Abubukar da alheri, ganin yadda ya ci amanar Kudu da shi kansa Wike din, wanda shi ya cancanta ya lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa a PDP."

Kara karanta wannan

Daga karshe: Dalilin ganawar Wike da Atiku, Tinubu, Peter Obi da Obasanjo a Landan ya fito

Kamata ya yi Wike ya bi Tinubu ko Peter Obi - inji Okechukwu

A ganin Okechukwu, kamata ya yi a ce Wike ya koma tsagin Tinubu ko kuma Peter Obi, rahoton Daily Post.

Ya kafa hujja da ganin yadda APC ke da dan takara mai kwarin gwiwa da karbuwa, da kuma LP mai dan takarar da ke da jama'ar da ke kaunarsa a yankinsu.

Ya kuma ce, har 'yan Arewa ba sa farin ciki da yadda Atiku ya yaudari 'yan yankin Kudu a zaben fidda gwanin da aka kammala.

Tsohon Shugaban Najeriya Obasanjo Ya Gana da Wike, Peter Obi da Wasu a Landan

A tun farko, a yau ne wasu hotuna suka karade kafafen sada zumunta, inda aka ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo tare da wasi jiga-jiga siyasar Najeriya a birnin Landan.

Rahoton da muke samu daga jaridar The Nation an cewa, ganawar ta hada dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Peter Obi da gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike da kuma gwamnonin jam'iyyar PDP uku.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Atiku Abubakar Ya Sa Labule da Gwamna Wike da Wasu Gwamnoni Uku a Landan

Gwamnonin da suka hallara a ganawar sun hada da: Samuel Ortom na jihar Benue, Seyi Makinde na jihar Oyo da kana da Okezie Ikpeazu na jihar Abia.

Asali: Legit.ng

Online view pixel