Tsohon Shugaban Najeriya Obasanjo Ya Gana da Wike, Peter Obi da Wasu a Landan

Tsohon Shugaban Najeriya Obasanjo Ya Gana da Wike, Peter Obi da Wasu a Landan

  • Rahoton da muke samu daga birnin Landan ya bayyana cewa, an yi wata ganawa ta sirri tsakanin Obasanjo da wasu jiga-jigan siyasar Najeriya
  • Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour na neman jawo gwamnan Ribas Wike zuwa jam'iyyarsu
  • Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin gwamna Wike na PDP da dan takarar jam'iyyar na shugaban kasa Atiku Abubakar

Landan, Burtaniya - A yau ne wasu hotuna suka karade kafafen sada zumunta, inda aka ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo tare da wasi jiga-jiga siyasar Najeriya a birnin Landan.

Rahoton da muke samu daga jaridar The Nation an cewa, ganawar ta hada dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Peter Obi da gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike da kuma gwamnonin jam'iyyar PDP uku.

Kara karanta wannan

Hotunan Mayakan Kasar Waje Masu Alaka Da Boko Haram Da Aka Kama A Benue

Hotunan ganawar Peter Obi da Wike da Obasanjo
Tsohon shugaban Najeriya Obasanjo ya gana da Wike, Peter Obi da wasu a Landan | Hoto: Punch Newspaper
Asali: UGC

Gwamnonin da suka hallara a ganawar sun hada da: Samuel Ortom na jihar Benue, Seyi Makinde na jihar Oyo da kana da Okezie Ikpeazu na jihar Abia.

Hotunan ganawar ta Landan sun kuma nuno tsohon gwamnan jihar Kuros Riba, Donald Duke da Sanata Olaka Nwogu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har yanzu dai ba a san me aka tattauna a cikin ganawar ba, amma ana kyautata zaton batu ne na zaben 2023 da shirinsa ya hada su.

Rikicin Atiku da Wike

Idan baku manta ba, ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin gwamna Wike da Atiku, tun bayan da Atiku ya zabi gwamna Okowa a matsayin abokin takara a zaben 2023.

Gwamnonin PDPn uku da tsohon gwamna Duke 'yan tsagin Wike ne, kuma sun dage dole PDP ta tsige shugaban jam'iyya Sanata Iyorchia Ayu da sauran jiga-jigai a Arewa kafin su goyi bayan Atiku a 2023.

Kara karanta wannan

Mu ba butulu bane: Tinubu ne zan gaji Buhari a 2023, Insha Allahu, Masari ya bayyana dalilai

Hotunan da muka samo daga jaridar Punch sun nuna jiga-jigan siyasar a hade, wanda ke nuna alamar wani abu a kasa tsakaninsu da dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi.

Zan Mika Jami’o’in Tarayya Ga Gwamnatin Jihohi, inji dan takarar PDP Atiku

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce zai sauya akalar rikon jami’o’in gwamnatin tarayya, inda zai ba gwamnatin jihohi ragamarsu.

Atiku ya bayyana haka ne a yau Litinin 22 ga watan Agusta a bikin bude taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyin Najeriya na 2022 da aka gudanar a Otal din Eko and Suites da ke Legas a Kudu maso Yamma.

Taron mai taken ‘Bold Transitions’ zai gudana ne har zuwa ranar 26 ga watan Agustan wannan shekarar, Channels Tv ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel