Dalilin da Yasa Na Gana da Tinubu, Atiku, Peter Obi da Obasanjo a Landan, Wike Ya Magantu

Dalilin da Yasa Na Gana da Tinubu, Atiku, Peter Obi da Obasanjo a Landan, Wike Ya Magantu

  • Sa'o'i bayan ganawar Wike da wasu jiga-jigan Najeriya, batun da suka tattauna a kai ya fito fili daga bakin gwamnan
  • A yau ne gwamnan ya dawo Najeriya, inda ya bayyanawa manema labarai dalilin ganawarsa da shugabannin
  • Ana takun saka tsakanin Atiku Abubakar da gwamna Wike tun bayan kammala zaben fidda gwanin shugaban kasa na PDP

Fatakwal, jihar Ribas - Gwamna Nyesom Wike na Ribas ya tabbatar ya bayyana yadda tawagarsa ta tattauna da dan takarar shugaban kasan APC Asiwaju Ahmed Bola Tinubu a yunkurin tabbatar da kawo sauyi a Najeriya.

Hakazalika, gwamnan ya tabbatar da ganawarsa da ‘yan takarar shugaban kasan PDP Atiku Abubakar da na jam'iyyar Labour Peter Obi hade da tsohon shugaban kasan Najeriya Olusegun Obasanjo a Landan, rahoton Punch.

Dakilin ganawar Wike da jiga-jigan Najeriya fito
Dalilin da yasa na gana da Tinubu, Atiku, Peter Obi da Obasanjo a Landan, Wike ya magantu | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ya yi karin haske ne a filin jirgin sama na Fatakwal da Omagwa a karamar hukumar Ikwerre ta jihar Ribas bayan dawowarsa daga Landan a yau Juma’a 26 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Atiku Abubakar Ya Sa Labule da Gwamna Wike da Wasu Gwamnoni Uku a Landan

Wike dai na tare da gwamna Samuel Ortom na Benue da Okezie Ikpeazu na Abia, wadanda aka gani tare a wasu hotuna a Landan, The Nation ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dalilin ganawar

Da yake bayyana dalilin ganawar tasu, Wike ya ce sam ba batu ne da ya shafi zallar siyasa ba, abin da suka sa a gaba shine yadda za a kawo sauya ingantacce a Najeriya.

Ya ce babban abin da suka fi mai da hankali a ganawar ta Landan shi ne sauya fasalin tattalin arzikin kasar, ganin cewa babu abin da ke aiki a Najeriya.

"Duk wani abu da muka tattauna akai yana da alaka da goben 'yan Najeriya. Ba batu ne da aka kebe ko yake magana a kan wani gungun mutane ba. Mun yi imani da cewa, duk abin da muke yi a yanzu, muna yin mai yiwuwa ne don goben 'yan Najeriya."

Kara karanta wannan

Atiku ya kade: Obasanjo ya gana da Peter Obi, Wike da wasu jiga-jigai a Landan

Wike ya kuma yi tsokaci da cewa, shugabanci ba lamari ne na mutum daya ba, ahali ko ko wasu daidaiku, batu ne da ya shafi makomar kasa.

Tsohon Shugaban Najeriya Obasanjo Ya Gana da Wike, Peter Obi da Wasu a Landan

A wani labarin, a yau ne wasu hotuna suka karade kafafen sada zumunta, inda aka ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo tare da wasi jiga-jiga siyasar Najeriya a birnin Landan.

Rahoton da muke samu daga jaridar The Nation an cewa, ganawar ta hada dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Peter Obi da gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike da kuma gwamnonin jam'iyyar PDP uku.

Gwamnonin da suka hallara a ganawar sun hada da: Samuel Ortom na jihar Benue, Seyi Makinde na jihar Oyo da kana da Okezie Ikpeazu na jihar Abia.

Asali: Legit.ng

Online view pixel