Atiku Abubakar Ya Gana Da Gwamna Wike da Wasu Gwamnoni Uku a Landan

Atiku Abubakar Ya Gana Da Gwamna Wike da Wasu Gwamnoni Uku a Landan

  • Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya gana da gwamna Wike na jihar Ribas a birnin Landan
  • Rahoto ya nuna cewa taron ya samu halartar gwamnonin PDP uku daga tsagin Wike yayin da Gwamnan Adamawa ke tare da Atiku
  • Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Wike ya sa labule da Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban kasa a APC

London - Taron da aka jima ana dakon gani tsakanin ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, da Gwamna Nyesom Wike, ya gudana daga ƙarshe a birnin Landan.

Vanguard ta ruwaito cewa har yanzu ba'a bayyana cikakken bayanin abin da taron jiga-jigan PDP biyu suka tattauna a taron ba, wanda ya gudana jiya Laraba.

Kara karanta wannan

Magidanci Mai Mata 4 Da 'Yaya 34 Sun yi Rijistan Zabe, Yace Atiku Duk Zasu Kadawa Kuri'u

Taron Atiku da Wike a Landan.
Atiku Abubakar Ya Gana Da Gwamna Wike da Wasu Gwamnoni Uku a Landan Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Amma wasu bayanai sun ce taron ya maida hankali kan lalubo hanyar sulhu a tsakanin su da kuma bukatar cigaban jam'iyyar PDP zuwa mataki na gaba.

Waɗan da suka halarci taron idan aka jingine Atiku da Gwamna Wike sun haɗa da gwamnan jihar Abiya, Okezie Ikpeazu, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da takwaran su na jihar Benuwai, Samuel Ortom.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku ya shiga taron tare da rakiyar gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri.

Awanni kaɗan bayan tsohon shugaban ƙasa, Chief Olusegun Obasanjo, da ɗan takarar shugaban kasa a inuwar Labour Party, Peter Obi, sun gana da Wike, sanna Atiku ya isa.

Wike zai taimaki Tinubu a 2023 - Masari

Wannan taron na zuwa ne kwanaki uku bayan gwamna Wike ya gana da ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Atiku ya kade: Obasanjo ya gana da Peter Obi, Wike da wasu jiga-jigai a Landan

Na hannun daman Tinubu, Alhaji Ibrahim Masari, ya ce suna da yaƙinin Wike zai taimaka wa takarar Tinibu ya samu nasara cikin sauki a 2023, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Masari, wanda yanzu haka yake tare da jagoran APC a Landan, ya ce duk da ƴan Najeriya sun karɓi Tinubu kuma zai ci zaɓe ko ba taimake shi ba, amma Bahaushe na cewa, "Ko kana da kyau ka ƙara da wanka."

A wani labarin kuma Sabuwar Matsala a PDP, Ɗan Takarar Gwamna Ya Fice, Ya Koma Bayan Wanda Yake So Ya Gaji Buhari a 2023

Tsohon ɗan takarar gwamnan Anambra, Valentine Ozigbo, ya tabbatar da ficewarsa daga PDP a wani taro jiya.

Ozigbo, ya ce ba zai iya raba jam'iyya tsakaninsa da Peter Obi ba, wanda ya kira ɗan uwansa, uban gidansa kuma jagora.

Asali: Legit.ng

Online view pixel