Bola Tinubu Shugaban Kasan Najeriya Na Gaba, Inji Gwamnan Su Buhari, Masari

Bola Tinubu Shugaban Kasan Najeriya Na Gaba, Inji Gwamnan Su Buhari, Masari

  • Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana kwarin gwiwarsa game da nasarar Bola Ahmad Tinubu a zaben 2023
  • Tinubu ne dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, yana fuskantar cece-kuce saboda zabo abokin takara musulmi
  • Kiristocin Arewa 'yan APC na ci gaba da shawarin wanda za su zaba a matsayin shugaban kasa a zaben 223 mai zuwa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Aminu Bello Masari, gwamnan jihar Katsina ya bayyana kwarin giwarsa kan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Masari ya bayyana karara cewa, Tinubu zai lashe zaben shugaban kasa a 2023 “Insha Allahu.”

Gwamnan ya yi wannan magana ne yayin hira da gidan talabijin na TVC, a jiya Laraba 24 ga watan Agusta.

Tinubu ne zai gaji Buhari, inji Masari
Bola Tinubu shugaban kasan Najeriya na gaba, inji gwamnan su Buhari, Masari | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Da mai gabatarwa ya tambaye shi game da dan takarar da yake sa ran zai ci zabe a 2023, Masari ya tamabaya:

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan Ganawar Wike Da Tinubu, Atiku Ya Nufi Landan Don Shawo Kan Gwamnan Na Rivers

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Waye ake dashi da ya fi shi a fagen siyasar Najeriya a yau?"

Da aka tambaye game da Peter Obi na Labour Party, Masari yace:

“Ban ma san shi ba. Me aka yi tsohon gwamnan Anambra? Ka je ka tambayi duk wani dan Katsina da sauran ’yan siyasa ka ji mutum nawa ne suka san Peter Obi?
"Muna magana ne akan dan takarar shugaban kasan Najeriyan da ya tsallake duk wani shinge - na kabilanci, addini, yanki da dai sauransu."

Game da Atiku da sauran 'yan takara

Jaridar ThisDay ta ruwaito cewa, Masari ya ce sam ba yadda za a yi Atiku ya ci zabe, saboda faduwa a jininsa take.

Game da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, Masari ya ce:

Kara karanta wannan

Hantar Atiku da PDP Ta Kada Bayan Samun Bayanin Zaman Tinubu da Wike a Landan

“Ina kallon Atiku a matsayin babban jigo karfi, amma karfin mu ya fi na shi kuma shi kansa ya san haka. Ya shahara wajen tsayawa takara haka nan ya shahara wajen shan kaye.”

Masari ya yi kaca-kaca da batun cewa, Atiku ne dan takarar da ya fi cancanta ya gaji Buhari a 2023, inda yace:

"An sha fadin hakan amma bai taba faruwa ba, don haka a yanzu ma ba zai faru ba."

Game da soyayyar 'yan Arewa ga Tinubu, Masari ya ce:

“Sun riga sun kamu da sonsa. Da farko dai Bola ba sabon mutum bane a siyasar Najeriya kuma mu Katsinawa mun san irin gudunmawar da Bola Tinubu ya bayar a zaben 2015 wajen kawo Muhammadu Buhari karagar mulki.
"Mun san irin kai kawo da ya yi a 2019 domin Muhammadu Buhari ya ci gaba da mulki, mu a nan Katsina ba masu butulu bane."

Tikitin Musulmi-Musulmi: Dogara da Babachir Sun Gana da IBB, Abdusalami a Minna

Kara karanta wannan

Masoyin Inyamurai ne: Jigon NNPP ya fadi abin da Kwankwaso ya shirya yiwa Inyamurai

A wani labarin, tsohon kakakin majalisar wakilai ta tasa, Yakubu Dogara da tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal na ci gaba da ganawa da manyan kasar saboda nuna adawarsu da tikitin Musulmi da Musulmi na APC.

Jam'iyyar APC ta tsayar da Boka Ahmad Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa, hakazalika Tinubu ya zabo Kashim Shettima a matsayin abokin gami a zaben 2023 mai zuwa.

Kiristoci a Najeriya, musamman kungiyar CAN sun nuna adawa da wannan lamari kasancewar Tinubu da Shettima gaba daya musulmai ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel