Tikitin Musulmi-Musulmi: Dogara da Babachir Sun Gana da IBB, Abdusalami a Minna

Tikitin Musulmi-Musulmi: Dogara da Babachir Sun Gana da IBB, Abdusalami a Minna

  • Jiga-jigan siyasar Arewa kuma kiristoci na ci gaba da neman shawari da kulla yadda za su kawo matsala ga APC
  • APC ta zabi musulmi a matsayin dan takarar shugaban kasa, Tinubu ya zabi Shettima a matsayin abokin gami
  • Babachir Lawal da Yakubu Dogara sun kai ziyara Neja, sun gana da tsoffin shugabannin Najeriya na mulkin soja

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Minna, Neja - Tsohon kakakin majalisar wakilai ta tasa, Yakubu Dogara da tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal na ci gaba da ganawa da manyan kasar saboda nuna adawarsu da tikitin Musulmi da Musulmi na APC.

Jam'iyyar APC ta tsayar da Bola Ahmad Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa, hakazalika Tinubu ya zabo Kashim Shettima a matsayin abokin gami a zaben 2023 mai zuwa.

Kiristoci a Najeriya, musamman kungiyar CAN sun nuna adawa da wannan lamari kasancewar Tinubu da Shettima gaba daya musulmai ne.

Kara karanta wannan

Mu ba butulu bane: Tinubu ne zan gaji Buhari a 2023, Insha Allahu, Masari ya bayyana dalilai

Jiga-jigan kiristan Arewa na shawarin goyon bayan Kwankwaso, Obi ko Atiku
Tikitin Musulmi-Musulmi: Dogara da Babachir Sun Gana da IBB, Abdusalami a Minna | Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Babachir da Dogara sun samu rakiyar tsohon mataimakin gwamnan jihar Kogi, Simon Achuba, inda suka gana da Janar Ibrahim Ibrahim Badamasi Babangida a gidansa da ke Hilltop a Minnan jihar Neja.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakazalika, sun kuma ziyarci tsohon shugaban Najeriya tsohon shugaban kasa Janar Abdusalami Abubakar, Tribune Online ta ruwaito.

Kiristocin Arewa na adawa da tikitin musulmi da musulmi

A baya kadan ne suka yi taro da kungiyar Kiristocin Arewa na jam’iyyar APC a Abuja inda wakilai daga jihohi 19 na Arewa hadi da Abuja suka nuna adawa da tsarin APC, rahoton The Guardian.

Majiya daga tushe ta shaidawa jaridar cewa, Babachir, Dogara da sauran shugabannin Kiristocin Arewa a APC, “suna shawari kafin yanke shawarin karshe kan ‘yan takarar shugaban kasan da za su marawa baya gabanin zaben 2023.”

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan Ganawar Wike Da Tinubu, Atiku Ya Nufi Landan Don Shawo Kan Gwamnan Na Rivers

Majiyar ta kuma shaida cewa :

"A yanzu dai zabi ne tsakanin Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP, Rabi'u Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP da Peter Obi na jam'iyyar Labour."

Kar a Wani Sako NNPP a Hayaniyar Shekarau da Kwankwaso, Inji Shugaban NNPP

A wani labarin, shugaban jam'iyyar NNPP na kasa, farfesa Rufa’i Alkali, ya ce jam’iyyar ba zai yiwu a jefa jam'iyyar cikin cece-kuce ba saboda yunkurin ficewar Shekarau daga cikinta.

Shekarau, wanda tsohon dan APC ne ya zama jigon NNPP cikin kankanin lokaci tun bayan komarsa jam'iyyar a watan Mayun bana, Daily Nigerian ta ruwaito.

A ranar Litinin, 22 ga watan Agusta ne Mallam Shekarau ya ayyana ficewarsa daga NNPP saboda rashin ba magoya bayansa gatan da ya cancanta a jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel