Hantar Atiku da PDP Ta Kada Bayan Samun Bayanin Zaman Tinubu da Wike a Landan

Hantar Atiku da PDP Ta Kada Bayan Samun Bayanin Zaman Tinubu da Wike a Landan

  • ‘Dan takaran APC a zaben 2023, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da mutanensa sun yi taro da Gwamna Nyesom Wike a boye a Kasar Ingila
  • An fahimci cewa an tattauna da Nyesom Wike ne a kan yadda zai taimakawa jam’iyyar APC a zaben shugaban Najeriya da za ayi a badi
  • Kowane bangare ya zo da mutum uku inda Gwamnoni hudu (na Ekiti, Legas, Oyo, Benuwai) suka wakilci tsagin Bola Tinubu da na Wike

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

London - Zaman da aka yi a birnin Landan a kasar Ingila tsakanin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Nyesom Wike ya tada hankalin jam’iyyar PDP.

Rahoton Daily Trust na ranar Laraba, 24 ga watan Agusta 2022, ya bayyana cewa wannan zama da aka yi ya birkita PDP da ‘dan takaranta na zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Taron NBA: Abin da Atiku, Obi suka fada, yayin da aka nemi Kwankwaso aka rasa

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa a wannan zama da aka yi a ranar Litinin a kasar Ingila, an tattauna kan abin da ya shafi takarar Bola Tinubu a zaben 2023.

Kamar yadda rahoton ya nuna, mutane shida suka yi wannan zama. Gwamna Wike ya kawo mutum uku daga bangarensa, shi ma Tinubu ya kawo mutum uku.

Taro ya yi kyau inji wata majiya

Wani wanda yake bangaren Bola Tinubu ya tabbatar da cewa zaman ya haifar da da mai ido.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daga bangaren ‘dan takaran na APC akwai Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu sai kuma Mai girma Kayode Fayemi mai shirin barin mulkin jihar Ekiti.

Wike a Fatakwal
Nyesom Wike tare da Gwamnan Legas Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

A gefe guda, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai da kuma Gwamnan jihar Oyo watau Seyi Makinde ne suka wakilci tsagin Wike a wajen wannan zama.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Wike Ya Sha Alwashin Ganin-Bayan ‘Yan PDP a Ribas da ke tare da Atiku

Wani tsohon Ministan da ke tsagin Wike ya shaida cewa babu wani laifi don sun gana da Tinubu domin a cewarsa, Atiku ma ya hadu da gwamnonin APC.

Me aka tattauna a zaman?

Abin da aka tattauna a taron shi ne ko Gwamnan na Ribas zai fice daga PDP ko kuma za iyi zamansa a jam’iyyar, amma ya taimakawa APC a zabe mai zuwa.

Irinsu Sanata Adeseye Ogunlewe sun ba Wike shawarar ya bar jam’iyyar PDP domin ba a ganin darajarsa a nan, ya fada masa ya hada-kai da su a tafiyar APC.

Da aka tuntubi Mai magana da yawun Atiku Abubakar, Paul Ibe kan batun, ya ki cewa komai. Haka zalika an nemi jin ta bakin APC, amma duk ba a dace ba.

Ina Wike ya sa gaba?

Kuna da labari tun da Gwamnan Ribas, Nyesom Wike ya sha kashi a zaben tsaida ‘dan takaran shugaban kasa a hannun Atiku Abubakar, aka rasa gane kan shi.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Gwamna Ya Fadawa Atiku Abin da Zai Yi Idan Yana Son Cin Zabe

Wike ya hadu da Peter Obi mai neman takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar LP. Sai ga shi yanzu ana ji cewa ya gana da ‘dan takaran APC a birnin Landan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel