Kwankwaso Masoyin Inyamurai Ne, Inji Wanda Ya Assasa Jam’iyyar NNPP

Kwankwaso Masoyin Inyamurai Ne, Inji Wanda Ya Assasa Jam’iyyar NNPP

  • Jigon da ya assasa jam'iyyar NNPP ya fito ya yi magana, ya ce ya gamsu da zaben da NNPP ta yi a zaben fidda gwaninta
  • Boniface Aniebonam ya yi tsokaci da cewa, Kwankwaso mutum ne mai kaunar al'ummar Kudu maso Gabas
  • Jam'iyyun siyasa da jiga-jigansu na ci gaba da tallata 'yan takarar shugaban kasa yayin da 2023 ke kara karatowa

Jihar Legas - Ma'assasin jam'iyyar NNPP Boniface Aniebonam ya ce jam'iyyar bata yi zaben tumun dare ba da ta zabi Rabiu Kwankwaso a matsayin dan takarar shugaban kasanta a 2023.

Ya kuma bayyana cewa, Kwankwaso masoyi ne ga kabilar Igbo da duk al'ummar Kudu maso Gabashin Najeriya, Premium Times ta ruwaito.

Jagoran na NNPP ya bayyana hakan ne a yau Talata 23 ga watan Agusta a jihar Legas a wani taron da aka shirya na kaddamar da shirin NNPP karkashin Prime Maritime Project (PMP).

Kara karanta wannan

Kai mayaudari ne: Shekarau ya dira kan Kwankwaso, ya fasa kwai kan maganar sauya sheka

Kwankwaso masoyin 'yan Kudu maso Gabas ne, inji jigon NNPP
Kwankwaso masoyin Inyamurai ne, inji shugaban jam'iyyar NNPP | premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya ce, daya daga cikin abubuwan da NNPP za ta sa a gaba idan ta lashe zaben 2023 shi ne harkar da ta shafi ruwa, mazaunin kabilar Igbo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, Inyamurai da dama na harkar shige da ficen kaya ta ruwa, don haka akwai bukatar su zabi Kwankwaso domin habaka wannan sana'a tasu.

A cewarsa:

“Dan takarar shugaban kasa na yana kabilar Igbo sosai. Idan aka zabi Kwankwaso matsaloli da dama za su samu mafita.”

Ya kuma bayyana cewa, jam'iyyar NNPP na shirin kawo sauyi mai kyau ga al'ummar kasar nan baki daya, musamman yankin Igbo.

Burinmu gina Najeriyar da kowa zai yi alfahari da ita

Da yake nasa jawabin, shugaban NNPP na kasa Rufai Alkali yace manufar jam'iyyar shi ne gina Najeriyar da kowa zai mora, ya kuma yi alfahari da ita.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Ni tsohon ministan tsaro ne, ni zan iya gyara matsalar tsaron Najeriya

Ya kuma ce, jam’iyyar a shirye take ta habaka tare da gyara fannin tattalin arziki, tsaro, yakar fatara da sauran matsalolin Najeriya, TheCable ta ruwaito.

Ya kara da cewa:
“Muna kallon Najeriya ne ilahirinta. Kasar da za ta tafi da kowa, babu wani yanki da za a mayar saniyar ware. NNPP jam’iyyar siyasa ce mai saurin girma a Najeriya.”
“Muna bukatar samar da ingantacciyar Najeriya ga ‘ya’ya da jikokinmu kuma abin da NNPP nufi yi kenan, sabuwar jam’iyya, sabuwar fuska, sabuwar alkiblar ciyar da kasa gaba."

Dalilin da yasa na fice daga NNPP, na raba kaina da tafiyar Kwankwaso, bayanin Shekarau

A wani labarin, bayan sauka da motar jam'iyyar NNPP mai alama kayan marmari, Mallam Ibrahim Shekarau ya bayyana dalilan da suka sa yi watsi da jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.

Sheakau dai shi ne sanata mai wakiltar Kano tsakiya a majalisar dattawa, kuma ya fice daga APC bayan rasa tikitin komawa takara, inda ya koma NNPP aka bashi tikitin.

Kara karanta wannan

Rikicin Atiku Da Wike: PDP Za Ta Rasa Mambobi Da Dama A Yayin Da Jerry Gana Yayi Barazanar Fita Daga Jam'iyyar

Shekarau ya bayyana cewa, yanke fice daga NNPP ne biyo bayan hana magoya bayansa foma-fomai tsayawa takara a zaben 2023 mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel