2023: Magoya Bayan APC Da PDP 27,000 Sun Sauya Sheƙa Zuwa Labour Party A Wata Jihar Arewa

2023: Magoya Bayan APC Da PDP 27,000 Sun Sauya Sheƙa Zuwa Labour Party A Wata Jihar Arewa

  • Wasu yan jam'iyyar Peoples Democratic Party da All Progressives Congress sun fita daga jam'iyyunsu a Jihar Nasarawa
  • Mambobin jam'iyyar da aka ce sun fi 27,000 sun bar jam'iyyunsu sun koma Labour Party a jihar
  • A cewar shugaban jam'iyyar LP na Nasarawa, za a tarbi sabin yan jam'iyyar a hukumance a watan Satumban 2022

Nasarawa - A yayin da jam'iyyun siyasa ke shirin tunkarar babban zaben shekarar 2023, dubban yan Najeriya sun fice daga PDP da APC sun koma Labour Party a Nasarawa.

The Punch ta rahoto cewa tsaffin mambobin jam'iyyar mai mulki da mai hamayya kimanin 27,000 sun bar jam'iyyunsu sun dawo Labour Party.

Labour Party
2023: Mambobin APC Da PDP 27,000 Sun Koma Labour Party A Nasarawa. Hoto: Francis Okechukwu.

An kuma gano cewa tuni an fara shirin tarbar wadanda suka shigo jam'iyyar ta Labour Party a makon farko na watan Satumba.

An sanar da hakan ne yayin kaddamar da sabon ofishin Labour Party da matasa da mata suka bada a garin Agyaragu, karamar hukumar Obi ta jihar Nasarawa da shugaban jam'iyyar na jihar, Alexander Emmanuel ya yi.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Duk da Kokarin Sasanci, An Garkame Otal da Gidajen Mai na Mutanen Atiku a Ribas

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Emmanuel ya ce baya ga wadanda sabbin yan jam'iyyar, akwai magoya bayan jam'iyyar kimanin miliyan daya daga kungiyoyi 56 a kananan hukumomi 13 a jihar.

Kalamansa:

"Wadannan sabbin mutanen 27,000 sun nuna sha'awar shiga jam'iyyar mu ne cikin makonni biyu da suka gabata. Bayan tattalin mutane miliyan daya da aka yi a karamar hukumar Lafia don dan takarar shugaban kasarmu, Peter Obi, ne suka taho suka ayyana goyon bayansu ga jam'iyyar mu kuma an shirin tarbarsu a satin farkon Satumba.
"A yau, muna Agyaragu ne domin kaddamar da ofishin jam'iyya wanda matasa da mata na garin suka bada ta hanyar kungiyar tallafi ta Peter Obi.
"Kana iya ganin yadda mutane suka fito cikin kankanin lokaci. Muna murna da irin goyon bayan da muke samu a kullum. Ina kyautata zaton jam'iyyar LP za ta ci zaben shugaban kasa na 2023, da gwamna da sauran zabuka."

Kara karanta wannan

Jiga-Jigai da Mambobin PDP Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC, Shugabar Mata Ta Rungume Su a Kaduna

Wasu daga cikin wadanda suka sauya sheka sun bayyana dalilansu

Wasu daga cikin matasan da suka watsi da tsaffin jam'iyyunsu suka koma Labour Party sun fada wa Legit Hausa dalilan da yasa suka fice.

Daya daga cikinsu Mohammed Ogba wanda tsohon magoyin bayan APC ne ya ce jam'iyya mai mulki a kasar bata cika musu alkawurran da ta dauka ba a 2015 da 2019 sai dai kullum bada uzuri yana mai cewa an yaudare su.

Kalamansa:

"Gaskiya ba a cika mana alkawarin da aka dauka mana ba, tattalin arziki ya tabarbare, babu tsaro, matasa ba su da ayyukan yi kullum sai sabbin matsaloli ke bullowa.
"Kusan shekaru takwas amma har yanzu babu wani abin a zo a gani da gwamnatin tarayya da na jiha ta yi da ya inganta mana rayuwa kamar yadda aka mana alkawari."

Shi kuma Oseni Dauda, tsohon dan PDP ya ce shi da abokansa da dama sun yi watsi da PDPn saboda ita ma bata da banbanci da APC.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Shugaban APC Na Jiha Ɗaya Ya Rasa Muƙaminsa, An Kore Shi Daga Jam'iyyar

"Duk kusan halinsu daya, idan ka lura za ka ga suna ta sauya sheka tsakaninsu don haka mu yanzu mun gaji da su, za mu gwada sabuwar jam'iyya."

Da aka masa tambaya ko menene dalilin da yasa ya ke ganin Labour Party ce za ta kawo irin canjin da matasan ke nema, ya ce:

"Idan ka lura Labour Party tafiya ce ta matasa don haka ina kyautata zaton ba za su ki cika wa yan uwansu matasa alkawari ba, ko dan takarar shugaban kasar mu, Peter Obi ya ce so ya ke ya kwace jam'iyya ya bawa matasa."

Ka Ja Kunnen Magoya Bayan Ka, Tinubu Ya Gargadi Peter Obi Kan Yada Labaran Karya

A wani rahoton, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Asiwaju Bola Tinubu, ya bukaci takwararsa na Labour Party, Mr Peter Obi, ya ja kunnen magoya bayansa don su dena yada karya, makirci da aibanta shi da sauran yan takara.

Kara karanta wannan

Rikicin Atiku Da Wike: PDP Za Ta Rasa Mambobi Da Dama A Yayin Da Jerry Gana Yayi Barazanar Fita Daga Jam'iyyar

Tinubu, cikin sanarwar da direktan watsa labaransa, Mr Bayo Onanuga ya fitar, ya bukaci Obi ya ja kunnen magoya bayansa kuma ya bari zaben 2023 ya zama kan batutuwan da za su bunkasa kasa, cigaba da kwanciyar hankalin Najeriya, yana gargadin "karya da yada maganganu marasa tushe za ba su saka a ci zabe ba."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164