Ka Ja Kunnen Magoya Bayan Ka, Tinubu Ya Gargadi Peter Obi Kan Yada Labaran Karya

Ka Ja Kunnen Magoya Bayan Ka, Tinubu Ya Gargadi Peter Obi Kan Yada Labaran Karya

  • Akwai yi wa juna kallon hadarin kaji tsakanin bangaren jam'iyyar APC mai mulki da jam'iyyar hamayya mai tasowa ta Labour Party
  • Kungiyar yakin neman zaben Bola Tinubu ta zargi magoya bayan Obi da yada labaran karya game da dan takarar na APC
  • Don haka ne ta fitar da sanarwa tana mai gargadi ga Obi ya ja kunnen magoya bayansa su dena yada karya don hakan ba alheri bane ga Najeriya

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya bukaci takwararsa na Labour Party, Mr Peter Obi, ya ja kunnen magoya bayansa don su dena yada karya, makirci da aibanta shi da sauran yan takara.

Tinubu
2023: Tinubu Ya Kai Karar 'Obi-dients' Wurin Peter Obi, Ya Ce Ya Ja Musu Kunne. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Tinubu, cikin sanarwar da direktan watsa labaransa, Mr Bayo Onanuga ya fitar, ya bukaci Obi ya ja kunnen magoya bayansa kuma ya bari zaben 2023 ya zama kan batutuwan da za su bunkasa kasa, cigaba da kwanciyar hankalin Najeriya, yana gargadin "karya da yada maganganu marasa tushe za ba su saka a ci zabe ba."

Kara karanta wannan

2023: Abin Da Yasa Na Ki Shiga APC Da PDP, Dan Takarar Shugaban Kasa Na AP

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce zaben kasar za ta yi armashi idan aka mayar da hankali wurin batutuwan da za su inganta rayuwar yan Najeriya da fito da su daga talauci a maimakon shirme irin na yan tasha wadanda ba su nufin kasar da alheri.

Mr Onanuga ya ce kungiyar yakin neman zaben Tinubu ta ga akwai bukatar yin kira ga Mr Obi ya ja kunnen magoya bayansa bayan bincike da gano labarin bogi da ke ikirarin shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya rubuta wa Tinubu wasika, yana cewa ya goyi bayan Peter Obi kuma ya kula da lafiyarsa.

Shugaban kasar Ghana, ta sahihin shafinsa na Twitter ya karyata rahoton a matsayin makirci an wasu da ke son yaudarar mutane.

"Ban rubuta wannan wasikar ga jagoran APC ba, kuma ban taba tunanin hakan ba. Ghana da Najeriya suna da alaka mai kyau na tsawon shekaru, kuma ba zan yi katsalandan a harkokin cikin gida da siyasar Najeriya ba," in ji Shugaba Akufo-Addo ta Twitter.

Kara karanta wannan

2023: Najeriya Ba Za Ta Zauna Lafiya Ba Idan Mulki Ya Tsaya A Arewa, In Ji PANDEF

Onanuga ya ce:

"Mun gano an fara wallafar labarin bogin kan wasikar Akufo-Addo ne a ranar 22 ga watan Yuni a wani shafin yan damfara, mai adireshin worldnews.space da sunan shafin kuma World of News.
"Nazarin abin da ke shafin ya nuna karara shafi ne na Biafra. Kungiyar goyon bayan Peter Obi ta sak yada labarin karyar a ranar - hakan hujja ne da ke nuna yan Biafra da magoya bayan Peter Obi duk daya ne.
"Shafin Facebook da shafin labaran duk suna cike da labaran bogi kan Bola Tinubu. Mun kawo matsayin da muka ganin ya kamata mu fada wa Mr Obi ya nuna jagoranci ya nesanta kansa da magoya bayansa da ke amfani da labaran bogi da karya a matsayin makamin gurbata tunanin yan Najeriya."

Laifin Tinubu Ne "Idan Amaechi Ya Koma PDP", Babban Jigon APC Ya Fasa Kwai

A wani rahoton, Chukwuemeka Eze, fitaccen jagora a jam'iyyar APC kuma na hannun daman Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri, ya ce a dora wa Bola Tinubu laifi idan Amaechi ya bar jam'iyyar.

Kara karanta wannan

"Na San Tinubu Sama Da Shekaru 50, Amma Ba Zan Iya Goyon Bayansa Ba", Tsohon Minista Mai Goyon Bayan Atiku

Eze yana magana ne kan wani rahoto da ke ikirarin cewa dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar yana zawarcin Amaechi, The Punch ta rahoto.

Idan za a iya tunawa Eze a baya-bayan nan ya kasance yana magana kan Amaechi kuma ya ce idan Amaechi ya shiga PDP, laifin Tinubu ne, wato dan takarar shugaban kasa na APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel