Mambobin PDP Sun Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC a kudancin jihar Kaduna

Mambobin PDP Sun Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC a kudancin jihar Kaduna

  • Shugabar matan jam'iyyar APC a shiyyar kudancin Kaduna ta karɓi sabbin masu sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP
  • Mambobin PDP da suka sauya sheka sun bayyana cewa akwai wasu ɗaruruwa da zasu biyo bayan su nan gaba kaɗan
  • Sauya sheka daga jam'iyya zuwa wata lamari ne da ya saba aukuwa a siyaasar Najeriya musamman idan zaɓe ya gabato

Kaduna - Yayin da babban zaɓen 2023 ke ƙara kusantowa, Shugabar matan APC a shiyyar kudancin Kaduna, Hon. Racheal Averik, ta karɓi masu sauya sheƙa 47 daga jam'iyyar PDP ranar Asabar.

Jaridar Punch ta tattaro cewa mafi yawan masu sauya sheƙan sun fito ne daga gundumar Arak, ƙaramar hukumar Sanga a jihar Kaduna.

Masu sauya sheka a Kaduna.
Mambobin PDP Sun Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC a kudancin jihar Kaduna Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Sun bayyana cewa sun yanke shiga APCe ne saboda yadda gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ke jawo mata da matasa a gwamnatinsa da kuma shugabanci nagari.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Shugaban APC Na Jiha Ɗaya Ya Rasa Muƙaminsa, An Kore Shi Daga Jam'iyyar

"Salon shugabancin mai girma gwamna da kuma fifita mata a gwamnatinsa na cikin dalilan da suka ƙara mana kwarin guiwar shiga jam'iyyar APC."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Kusan mambobi 230 zasu biyo bayan mu nan gaba kaɗan domin tabbatar. da jam'iyyar ta cigaba da jan zarenta a zaɓe har bayan 2023," inji su.

Gwamnatin El-Rufai ta tallafawa mata da matasa

Averik tare da rakiyar wasu jiga-jigan APC yayin karɓan masu sauya sheƙar, ta ce a shekaru Bakwai da gwamnatin El-Rufai ta shafe ta aiwatar da shirin tallafa wa mata/matasa da dama da kuma jawo su jiki ta hanyar ba su muƙamai.

Ta koka cewa shugabannin tsagin adawa PDP sun fi damuwa da neman ɗarewa madafun iko maimakon su taimaka wajen kimtsa wa da sa ido kan shugabannin gobe.

Shugabar matan ta ce:

Kara karanta wannan

Sanata, Yan Majalisun Jiha da Jiga-Jigan PDP Sama da 500 Sun Fice Daga Jam'iyyar

"Jam'iyya mai mulki ta samar da damamaki ga matasa, waɗan da suka samu kujeru masu gwaɓi a gwamnatin Malam El-Rufai kuma a yau, sun zama Miliyoniyoyi."

Ta kuma tabbatar wa masu sauya shekan cewa ba za'a nuna musu banbanci ba, inda ta roke su da su yi amfani da dabarunsu na siyasa wajen tabbatar da nasarar APC a 2023.

A wani labarin kuma Babbar Magana, Shugaban APC na jiha ɗaya ya rasa muƙaminsa, An kore shi daga Jam'iyyar

Shugaban APC reshen jihar Enugu, Ugo Agbalah, ya rasa ƙujerarsa, an kore shi daga jam'iyyar baki ɗaya.

Bayanai sun nuna cewa tuntuni ake tuhumar shugaban da rashin yin rijistar zama ɗan jam'iyya, lamarin da ake tafka mahawara a Kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel