Rikicin PDP: Duk da Kokarin Sasanci, An Garkame Otal da Gidajen Mai na Mutanen Atiku a Ribas

Rikicin PDP: Duk da Kokarin Sasanci, An Garkame Otal da Gidajen Mai na Mutanen Atiku a Ribas

  • Salon rikicin jam'iyyar PDP ya dauka sabon salo inda aka rufe otal, gidajen mai da wasu kasuwancin makusantan Atiku
  • Gwamna Wike ya fara barazanar garkame dukkan otal din da ake tarukan siyasa wadanda zasu iya tattara 'yan kungiyar asiri da masu miyagun lamurra a jihar
  • Bayan sa'o'i kadan da bada wannan sanarwa, jami'an tsaro sun dira wasu ota da mashaya ta makusantan Atiku inda aka garkame

Ribas - Rikicin jam'iyyar PDP ya dauka sabon salo tsakanin Atiku da Wike inda aka sanyawa wasu magoya bayan Alhaji Atiku Abubakar mummunan takunkumi a jihar Ribas.

Shugabannin jam'iyyar sun dinga kokarin ganin sun sasanta Gwamna Nyesom Wike, wanda ya rasa tikitin shugabancin kasa kuma ya sake asarar samun tikitin mataimakin kasa na jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Yadda Dogarin Minista Ya Lakadi Ma'aikata da 'Dan Jarida a Gidan Buhari

Wike in Rivers
Rikicin PDP: Duk da Kokarin Sasanci, An Garkame Otal da Gidajen Mai na Mutanen Atiku a Ribas. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

'Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP ya zabi Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta a matsayin abokin tafiyarsa, inda yace yafi jin dadin aiki da shi.

Bayan bayyana sunan Okowa a fili, Wike ya musanta kansa daga Atiku kuma ya fara shigewa manyan jam'iyyar APC, wadanda ba ziyara kadai suka kai masa ba, har kaddamar da ayyukan da yayi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A ranar Juma'a, kwamitin sasancin Atiku da Wike sun gana a Ribas. Duk da hakan, otal, gidajen mai da wasu kasuwancin makusantan Atiku duk an garkame su a jihar.

A cikin kwanakin nan, an samu hargitsa a Fatakwal bayan Wike ya ja kunnen wasu mazauna jihar kan zuwa otal, wurin shakawata da gidajen mayukan da ake zargin masu satar mai ne suka mallaka.

Gwamnan ya yi barazanar cewa mulkinsa zai rufe kowanne otal da ake amfani da su wurin tarukan siyasa da 'yan kungiyar asiri da sauran miyagun lamurra a jihar.

Kara karanta wannan

2023: Ka Maye Gurbin Shettima Da Kirista, Matasan APC Suka Fada Wa Tinubu

Bayan sa'o'i kadan da fadin hakan, jami'an tsaro sun kutsa mashayar Priscy dake fitaccen yankin Elekaha a Fatakwal, da wani otal dake tsibirin Eagle a babban birnin j9ihar tare da cafke wasu kwastomomi kafin su garkame wurin.

Otal din da mashayar duk mallakin Ikechi Chinda da Jones Ogbonda, wadanda makusantan Aystin Opara, tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai.

Opara da Wike sun saba fadan kasan kasa kan abinda ake kwatantawa da alakarsu da 'dan takara shugaban kasa na jam'iyyar PDP.

An garkame wani gidan mai mallakin Honarabul Chiyere Igwe, 'dan majalisar dake wakiltar mazabar Fatakwal ta biyu a majalisar wakilai kan zarginsa da satar mai.

Gwamnan daga bisani ya bayar da umarnin damke Igwe kan zarginsa da hannu a satar mai.

Gwamnan yayin bayar da umarnin yace, gwamnati zata tabbatar da ta ladabtar da mamallakan gidajen man domin ta bayyana kokarinta wurin hana satar mai a jihar.

Amma a yayin martani, Igwe wanda makusancin Opara ne yace an yi musu hakan ne saboda kusancinsu da Atiku, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Harin Jirgin kasa: 'Dan Uwan Budurwar da Shugaban Yan Bindiga Ke Kokarin Aurawa Kansa Ya Koka

Asali: Legit.ng

Online view pixel