Rikicin Atiku Da Wike: PDP Za Ta Rasa Mambobi Da Dama A Yayin Da Jerry Gana Yayi Barazanar Fita Daga Jam'iyyar

Rikicin Atiku Da Wike: PDP Za Ta Rasa Mambobi Da Dama A Yayin Da Jerry Gana Yayi Barazanar Fita Daga Jam'iyyar

  • Rikicin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya sake daukan sabon salo a yayin da bangarorin da ke rikici suka gaza yin sulhu
  • Kwamitin da aka kafa don yin sulhu tsakanin Atiku Abubakar da Gwamna Nyesom Wike ta gana a Port Harcourt, ranar Juma'a 19 ga watan Agusta
  • Farfesa Jerry Gana, mamba na tawagar Wike, amma, ya ce akwai yiwuwar ya fita daga jam'iyyar idan ba a warware rikicin ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Idan Atiku Abubakar da Gwamna Nyesome Wike na Jihar Rivers ba su mayar da takkubansu ba sun rungumi zaman lafiya, mambobi da dama na jam'iyyar PDP za su fice daga jam'iyyar gabanin babban zaben 2023.

Wike da PDP
Rikicin Atiku Da Wike: PDP Za Ta Rasa Mambobi Da Dama A Yayin Da Jerry Gana Yayi Barazanar Fita Daga Jam'iyyar. Hoto: Nyesom Wike and Atiku Abubakar.
Asali: Facebook

Daily Independent ta rahoto cewa tsohon ministan labarai kuma jagora na kwamitin sulhu a bangaren Wike, Farfesa Jerry Gana, ya yi gargadin cewa idan ba a warware matsalar jam'iyyar ba, gwamnan, da shi da wasu za su fita daga jam'iyyar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Legit.ng ta tattaro cewa a jawabin da ya yi wurin kaddamar da ayyuka a Port Harcourt, Jihar Rivers, Gana, ya yi kira ga yan Najeriya kada su yi asarar kuri'unsu kan APC domin ta gaza.

Ya ce:

"Muna son tabbatar muku cewa zamu warware matsalolin da ke PDP, idan hakan bai yi wu ba, wannan jagoran, gwamnan da ke nan, tare da dukkan mu, za mu fada wa yan Najeriya inda za a tafi. Ba yara bane su.
"Kada ku yi kuskuren asarar kuri'un ku ku zabi dayan bangaren. Kun san wadanda na ke nufi. Sun gaza, sun gaza sosai, don haka kada ku yi tunanin zuwa nan."

2023: Rikicin PDP Ya Dauki Sabon Salo, Gwamnoni Da Ke Goyon Bayan Wike Sun Gindayawa Atiku Sabbin Sharruda

A baya, gwamnonin PDP da ke biyaya ga gwamnan Rivers, Nyesom Wike, sun bada wasu sharruda ga dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar, kafin su mara masa baya a zaben 2023, kamar yadda aka rahoto.

A cewar Daily Independent, gwamnonin za su hadu da Atiku a karshen mako don tattaunawa kan matsalolin da ke adabar jam'iyyar.

Jaridar ta rahoto cewa daya daga cikin mambobin tawagar Gwamna Wike yana cewa duk ma abin da ya faru, sun amince babu wanda zai fita daga jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel