Yan Takara Biyar Da Suke Kan gaba Wajen Neman Kujerar Masari

Yan Takara Biyar Da Suke Kan gaba Wajen Neman Kujerar Masari

  • Bayan zaben fidda gwani na jam’iyyun siyasa daban-daban a jihar Katsina Hukumar INEC ta Fito da jerin sunayen yan takarar gwamna Na jihar guda 13
  • A cikin ’yan takarar gwamna 13 da jam’iyyunsu siyasa suka fitar a jihar Katsina guda biyar kadai ake ganin daya daga cikin su maye gurbin kujerar Masari
  • Jerin sunayen yan takara guda biyar dake kan gaba sun hada Dr Umar Dikko APC, Sanata Lado Yakubu PDP, Nura Khalil na NNPP, Imrana Jino na PRP da Ibrahim Zakkari na SDP

Jihar Katsina - Yan takarar gwamna 13 ne suka fito takara a zaben badi a jihar Katsina, bayan zaben fidda gwani na jam’iyyun siyasa daban-daban. Amma, biyar ne kawai daga cikinsu ake ganin za su yi fice a zaben. Rahoton The Nation

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fitar da jerin sunayen jam’iyyun siyasa 13 da ‘yan takararsu na zaben gwamna a jihar Katsina mai zuwa.

Kara karanta wannan

2023: Yadda Gwamnonin PDP da Jiga-jigan Jam’iyya Suka Yi Watsi da Atiku a Yola

Fafatawar maye gurbin kujerar Gwamna Aminu Bello Masari ya yi kamari, biyo bayan yadda aka gudanar da zabukan fidda gwani. A cikin ’yan takarar gwamna 13 da jam’iyyunsu siyasa suka fitar guda biyar ne kawai za a iya la’akari da su a matsayin ‘yan takarar gaske.

Katsina
Yan Takara Biyar Da Suke Kan gaba Wajen Neman Kujerar Masari FOTO THE NATION
Asali: UGC

Wadanda suka hada da

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dr Umar Dikko Radda na jam'iyyar APC, Sanata Lado Yakubu Darmake na jam'iyyar PDP, Nura Khalil na jam'iyyar New Nigerian Peoples' Party (NNPP), Imrana Jino na jam'iyyar Redemption Party. (PRP) da Ibrahim Zakkari na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).Rahoton LEADERHIP

Dikko Radda, APC:

Jama’a da dama na kallon dan takarar na jam’iyyar APC a matsayin wanda ke da kyakkyawar damar lashe zabe saboda lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar, ya kayar da wasu manyan yan takara. Hakan ya girgiza masana da dama da a yanzu suke ganin shi ne zai ci zabe.

Kara karanta wannan

Tsohon Hadimin Buhari Ya Kyale APC, Ya Yanki Fam din Takarar Gwamnan Kano

Radda, tsohon Darakta-Janar ne kuma Babban Shugaban Hukumar Bunkasa Kanana da Matsakaitan Masana’antu ta Najeriya (SMEDAN), ya kasance fitaccen dan siyasa, dan kasuwa, malami kuma ma’aikacin banki mai dimbin gogewar harkokin mulki a matakin kananan hukumomi, jihohi da tarayya na tsawon shekaru da dama. .

Lado Danmarke, PDP:

Sanata Lado Danmarke na jam’iyyar PDP shi ne kuma dan takara mai karfi wanda asalinsa ya sa ya samu goyon bayan jama’a, galibi daga tushe.

Sanatan daya taba zama dan majalisar wakilai kuma shugaban karamar hukumar Kankara ya bayar da gudunmawa matuka ga ci gaban jihar da kuma jam’iyyar PDP, wanda hakan ya sanya mi shi farin jini a tsakanin al’umma.

Imrana Jino, PRP:

Masu sukar jam'iyyar PRP na ganin jam'iyyar ta dogara ne da sunan da tayi abaya lokacin su tsohon gwamnan jihar kaduna Balarabe Musa. Hakan ya faru ne saboda dadewar da ta yi a arewa.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Wike Ya Fallasa Wadanda Su Ka Kitsa Masa Zagon-Kasa a Tafiyar PDP

Masu fashin baki na ganin cewa dan takarar na PRP ba zai yi wani tasiri sosai ba, dangane da takarar gwamna.

Ibrahim Zakari, SDP:

Wani dan takarar gwamna da masana ke fargabar ba zai yi tasiri sosai shi ne na SDP, Ibrahim Zakkari. Kwanan nan ya fice daga jam’iyyar NNPP ya karbi tikitin jam’iyyar SDP bisa zargin magudin a zaben fidda gwani na jam’iyyar NNPP.

Duk da haka, Zakkari ya shigo jam’iyyar SDP tare da fatan samun nasara a zaben badi.

Duk da cewa Zakkari dan siyasa ne mai cikakken bayani, amma manazarta ba su yi imanin cewa jam’iyyar tana da tsarin da zai iya amfani da shi wajen tabbatar da aniyarsa ba, domin har ya zuwa yanzu fafatawar da Gwamna Masari ya yi na neman ya gaji Gwamna Masari na fuskantar kalubale.

Nura Khalil, NNPP:

Dan takarar jam’iyyar NNPP, Nura Khalil, ya kasance fitaccen dan siyasar da ya shahara a jihar. Ya bar fagen siyasa a shekarar 2004 don maida hankali kan harkokinsa. Amma, ya sauya sheka ne a lokacin da ya bayyana sha’awar tsayawa takarar gwamna a Katsina a badi kuma hakan ya rage masa kwarjini a idon masu zabe.

Kara karanta wannan

Manyan Jami'an Gwamnati, Yan Siyasa Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Daurin Auren Diyar Sule Lamido

Khalil ya dawo ne a shekarar 2022 inda ya karbi tikitin takarar gwamna a jam’iyyar NNPP, tare da kwarin gwuiwar cewa zai lashe kujerar na daya.

Biyu Babu: Lawan Da Akpabio Ba Sa Cikin Yan Takarar Senata, INEC

Abuja - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce ba ta amince da saka sunan Sanata Ahmed Lawan matsayin ‘yan takarar senata a Yobe ta Arewa da Godswill Akpabio a matsayin dan takarar senata a Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma ba. Rahoton LEADERSHIP

Hukumar INEC ta ce bata dauki daya daga cikin mutanen biyu a matsayin yan takarar Sanata a zaben 2023 mai zuwa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel