Biyubabu: Lawan Da Akpabio Ba Sa Cikin Yan Takarar Senata, INEC

Biyubabu: Lawan Da Akpabio Ba Sa Cikin Yan Takarar Senata, INEC

  • Hukumar Zabe INEC ta ce ba ta amince da saka sunan Sanata Ahmed Lawan da Godswill Akpabio a matsayin yan takarar senata a yankunan su ba
  • Hukumar INEC ta ce zata yi amfani da kwafin fom din sunaye yan takara da jam'iyyu suka gabatar mata kafin ta rufe dandalin tantance sunaye
  • Form EC9 shine fom din sunayen yan takara da jam’iyyun siyasa ta mika wa INEC kuma sune a tashar INEC

Abuja - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce ba ta amince da saka sunan Sanata Ahmed Lawan matsayin ‘yan takarar senata a Yobe ta Arewa da Godswill Akpabio a matsayin dan takarar senata a Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma ba. Rahoton LEADERSHIP

Kara karanta wannan

Rikicin Atiku da Wike: Jam'iyyar PDP ta dage zaman NEC saboda ta'azzarar rikicin gida

Hukumar INEC ta ce bata dauki daya daga cikin mutanen biyu a matsayin yan takarar Sanata a zaben 2023 mai zuwa ba.

Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Festus Okoye, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata mai taken: ‘zarge-zarge dangane da tantance ‘yan takara a wasu gundumomin sanatoci da aka gabatar wa ‘yan jarida.

Lawan
2023 : Lawan Da Akpabio Ba Sa Cikin Yan Takarar Senata INEC FOTO PremiumTIMES
Asali: UGC

Okoye ya ce a matsayin shaida na rawar da Hukumar ta taka, tun da farko an gabatar da kwafin gaskiya na Form 9C da jam’iyyun suka shigar kuma Hukumar ta samu a ranar 17 ga Yuni, 2022 lokacin da aka rufe dandalin tantance sunaye.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Domin a fayyace, ya ce Form EC9 shine fom din sunayen yan takara da jam’iyyun siyasa ta mika wa INEC kuma sune a tashar ta INEC.

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Fuskanci Matsala Tun Yanzu, Ana Hure Kunnen Darektan Kamfen da Ya Zaba

Ya ce an yi nuni a fili a kan sunan fom din da aka karba a ranar 17 ga watan Yuni, 2022 lokacin da aka rufe tashar.

Dalibin Makarantar Sakandare Ya Kera Na'urar Mutum Mutumi Da Kansa A Jihar Kano

A wani labari kuma, Isah Barde, matashi dan shekara 17 da ya kammala karatunsa na sakandare a jihar Kano, ya kera Na'urar Mutum Mutumi daga tarkace, inda ya yi amfani da kwali, bututu, ledodi, moto, aluminum, da dai sauransu, a matsayin kayan aikin sa. rahoton Daily Trust

Isah yayi nazarin karantar fasahar kere-kere da zama kwararre a harkar leken asiri, duk da matsalar kudi da ke gabansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel