Tsohon Hadimin Buhari Ya Kyale APC, Ya Yanki Fam din Takarar Gwamnan Kano

Tsohon Hadimin Buhari Ya Kyale APC, Ya Yanki Fam din Takarar Gwamnan Kano

  • Sha’aban Ibrahim Sharada mai wakitar Karamar Hukumar Birni a Jihar Kano ya shiga jam’iyyar ADP
  • Hon. Sharada zai yi takarar kujerar gwamnan Kano a karkashin ADP bayan shan kashi jam’iyyar APC

Kano - Zaman Sha’aban Ibrahim Sharada a jam’iyyar APC ya zo karshe. Jaridu da-dama, daga ciki akwai Daily Trust, sun kawo wannan rahoto.

Honarabul Sha’aban Ibrahim Sharada ya sauya-sheka daga APC mai mulki ne bayan tsawon lokacin bangarensu na G7 suna rigima da gwamnati.

Sharada mai wakiltar Birnn Kano a majalisar wakilan tarayya ya shiga jam’iyyar adawa ta ADP. Shigarsa jam’iyyar ke da wuya, ya samu takara.

Kamar yadda Leadership ta kawo rahoto a yamman Talata, 16 ga watan Agusta 2022, Sharada za iyi takarar gwamnan Kano a jam’iyyar da ya shiga.

Kara karanta wannan

2023: Bayan Atiku, Tinubu Shima Yana Zawarcin Shekarau, Za Su Gana Ranar Laraba

Wanda zai zama abokin takarar Sha’aban Ibrahim Sharada a karkashin inuwar Action Democratic Party a zabe mai zuwa shi ne Rabiu Bako.

Babu maganar shiga NNPP

Rahoton da jaridar ta fitar ya nuna cewa an yi ta tunanin Sharada zai shiga jam’iyyar nan ta NNPP, sai su hadu da tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon Hadimin Buhari
Sha'aban Sharada tare da Shugaban kasa Hoto: Malam Sha'aban Ibrahim Sharada For Member House Of Representative
Asali: Facebook

A karshe dai ‘dan siyasar ya yi watsi da batun shiga jam’iyya mai kayan marmari, ya zabi ADP.

Da wannan cigaba da aka samu, masu neman gwamna a Kano sun karu. Jam’iyyun APC, PDP, NNPP, PRP, ADC, da ADP duk su na da manya ‘yan takara.

G7 ta watse a Kano?

Shugaban kwamitin leken asiri na majalisar tarayyar kasar ya rasa gindin zama ne a APC bayan Nasiru Gawuna da Murtala Sule Garo sun samu tikiti.

Baya ga haka, ‘dan majalisar ya sha kasa a karar da ‘yan taware na G7 suka shigar a kan jam’iyyar APC ta reshen Kano, su na kalubalantar shugabanninta.

Kara karanta wannan

Bayan Wata 4 rak a Ofis, An Soma Yunkurin Raba Adamu da Shugabancin APC

Sauran ‘yan tafiyar G7 irinsu Barau Jibrin da Ibrahim Shekarau sun sake samun takarar kujerar Sanatansu a karkashin jam’iyyun APC da kuma NNPP.

Makomar mukarraban Buhari

Kwanaki kun samu labari wasu na-kusa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari sun nemi yin takara a jam'iyyar a APC, sai ga shi ba su iya samun tikiti ba.

A cikin wadanda suka sha kashi a zaben fitar da gwani na APC har da ‘danuwan shugaban kasar, hadimansa da kuma tsofaffin masu ba shi shawara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel