2023: Yadda Gwamnonin PDP da Jiga-jigan Jam’iyya Suka Yi Watsi da Atiku a Yola

2023: Yadda Gwamnonin PDP da Jiga-jigan Jam’iyya Suka Yi Watsi da Atiku a Yola

  • Atiku Abubakar ya karbi ‘ya ‘yan jam’iyyar APC da suka sauya-sheka zuwa PDP a jihar Adamawa
  • An yi taron yi wa ‘Yan siyasar wankan tsarkin shigowarsu jam’iyyar PDP a garin Yola a ranar Litinin
  • Gwamnan Adamawa kurum aka gani a wajen gangamin, mafi yawan ‘Yan NWC duk ba su halarta ba

Adamawa - Rashin ganin gwamnonin jihohi da kuma shugabannin jam’iyyar PDP a garin Yola a jihar Adamawa ya haska rigimar da ake fama da ita.

Atiku Abubakar ya shiga jiharsa ta Adamawa a makon nan, Vanguard ta rahoto cewa ziyarar ta rage karfin gwiwar yakin zaben ‘dan takarar na 2023.

A ranar Litinin aka shirya gangamin siyasa inda Alhaji Atiku Abubakar ya karbi wasu magoya bayan jam’iyyar APC da suka koma PDP a garin Yola.

Kara karanta wannan

Masu Neman Kujerun APC Sun Tada rikici, Sun bukaci Jam’iyya ta Biya su Kudinsu

Mutane sun yi tunanin cewa za a ga gwamnonin jam’iyyar APC da ‘yan majalisar NWC na kasa da-dama a wajen taron, amma ba hakan aka yi ba.

Rahoton yace baya ga Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, babu wani Gwamna da aka gani a gangamin. Sai kuma mutum hadu a ‘yan kwamitin NWC.

‘Dan takarar mataimakin shugaban kasa a PDP, Ifeanyi Okowa yana wajen taron. Shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu ya jagoranci ‘yan majalisarsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Atiku
Atiku da Gwamnan Adamawa Hoto: @Atiku
Asali: Twitter

Su wanene suka je taron?

Jagororin PDP na kasa da aka gani a taron Yola sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, Sanata Adamu Maina da Sanata Dino Melaye.

Sai kuma tsofaffin gwamnoni na Adamawa da Neja; Boni Haruna da Muazu Babangida Aliyu.

Peter Obi zai raba PDP?

Ana wannan sai aka ji labari Peter Obi mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP ya sake yin zama da Gwamnan Ribas, Nyesom Wike a Fatakwal.

Kara karanta wannan

Tsohon Hadimin Buhari Ya Kyale APC, Ya Yanki Fam din Takarar Gwamnan Kano

Sauran wadanda aka yi zaman da su sun hada da; Ibrahim Danwambo; Samuel Ortom; Okezie Ikpeazu; Donald Duke, Mohammed Adoke da sauransu.

Kusan duka wadannan ‘yan siyasa ba su goyi bayan Atiku Abubakar ya zama ‘dan takarar shugaban kasa ba, duk sun marawa Nyesom Wike baya ne

Kwankwaso ya nada kakaki

A wata sanarwa da ta fito, an ji labari Rabiu Kwankwaso ya zabi Abdulmumin Jibrin da Barr. Ladipo Johnson a matsayin kakakin kamfensa a NNPP

Hon Abdulmumin Jibrin da Barr. Ladipo Johnson za su kalubalanci Festus Keyamo na APC da kuma Dino Melaye da Daniel Bwala a PDP a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel