Manyan Jami'an Gwamnati, Yan Siyasa Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Daurin Auren Diyar Sule Lamido

Manyan Jami'an Gwamnati, Yan Siyasa Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Daurin Auren Diyar Sule Lamido

  • A ranar Asabar, 13 ga watan Agusta ne aka kulla aure tsakanin diyar tsohon gwamnan jihar Jigawa, Surayya Sule Lamido da angonta Yazid Dan Fulani
  • Jihar Jigawa ta yi cikar kwari domin manyan masu fada aji a kasar da yan siyasa sun yiwa Lamido kara wajen halartan daurin auren
  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, mataimakinsa, Ifeanyi Okowa duk sun halarci daurin auren da aka yi a garin Bamaina

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jigawa - Manyan yan siyasa da jami’an gwamnati sun yiwa garin Bamaina, mahaifar tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido tsinke a ranar Asabar, 13 ga watan Agusta, domin halartan daurin auren diyarsa, Surayya.

Daga cikin manyan tawagar jam’iyyar PDP da suka halarci daurin auren akwai dan takarar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar da abokin takararsa, Sanata Ifeanyi Okowa da kuma gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Aminu Tambuwal.

Kara karanta wannan

Kakar Abba Gida-Gida, Dan Takarar Gwamna Na Jam'iyyar NNPP A Kano Ta Rasu

Surayya, Sule Lamido da angonta
Manyan Gwamnati, Yan Siyasa Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Daurin Auren Diyar Sule Lamido Hoto: fashionseriesng
Asali: Instagram

Shugaban kwamitin amintattu na PDP, Sanata Walid Jibril, shugaban jam’iyyar na kasa, Dr. Iyorchia Ayu da sauran yayan kwamitin uwar jam’iyya duk sun halarci daurin auren, jaridar Thisday ta rahoto.

Tambuwal ya samu rakiyar mataimakinsa kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar, Alhaji Saidu Umar (Mallam Ubandoman Sokoto) da Hon. Sagir Bafarawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran manyan yan siyasa da suka halarci daurin auren sune gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, tsohon mataimakin shugaban kasa, Architect Muhammad Namadi Sambo, tsohon mai ba kasa shawara kan tsaro Aliyu Muhammad Gusau (mai ritaya).

Sai kuma tsohon ministan ayyuka na musamman, Kabiru Tanimu Turaki (SAN) da takwaransa na harkokin yan sanda, Alhaji Adamu Maina Waziri.

Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Alhaji Ahmed Adamu Muazu da takwarorinsa na jihar Kaduna, Alhaji Ahmad Makarfi, da Alhaji Mukhtar Yero da Alhaji Ibrahim Dankwambo duk sun hallara.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike ya Kai Atiku da Tambuwal Kotu, yace Shi ne Asalin ‘Dan takaran PDP

Tsoffin yan majalisa da suka halarci daurin auren sun hada da Sanata Abdul Ningi, Sanata Lado Danmarke da Hon. Farouk Aliyu, jigon jam’iyyar APC na kasa.

Sarakunan gargajiya daga Jigawa da jihohin da ke makwabtaka duk sun halarci daurin auren.

Diyar Tsohon Zababben Gwamnan Zamfara Ta Shiga Daga Ciki, Ya Yi Mata Kyautar Dankareriyar Sarka A Bidiyo

A wani labarin, mun ji cewa kyakkyawar diyar tsohon zababben gwamnan jihar Zamfara, Mukhthar Idris Koguna mai suna Islam ta shiga daga ciki.

A cikin wani bidiyo da ya yadu a shafukan soshiyal midiya, an gano zukekiyar amaryar cikin wata hadaddiyar doguwar riga irin na amaren zamani, kanta lullube da mayafi wanda aka jerawa duwatsu.

Abun birgewa kuma shine mahaifin nata da kansa ne ya daura mata wani dankararren sarkan wuya mai kyau domin cika adonta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel