2023: Gwamna Wike Ya Fallasa Wadanda Su Ka Kitsa Masa Zagon-Kasa a Tafiyar PDP

2023: Gwamna Wike Ya Fallasa Wadanda Su Ka Kitsa Masa Zagon-Kasa a Tafiyar PDP

  • Nyesom Wike ya bayyana cewa ‘Yan siyasan jihar Ribas ne suka juya masa baya a jam’iyyar PDP
  • Gwamnan yake cewa wadanda suka fadi zaben fitar da gwani na Gwamna suka yi masa bukulu
  • Wike yace wadannan mutane ne ke bakin-cikin ya zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa

Rivers – Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya zargi dattawan jam’iyyar hamayya ta PDP da shirya masa zagon-kasa wajen samun takara a zaben 2023.

A ranar Litinin, 15 ga watan Agusta 2022, Vanguard ta rahoto Nyesom Wike yana zargin wadanda suka nemi takarar gwamnan Ribas da ganin bayansa.

Gwamnan ya yi magana ne a wani jawabi da kakakinsa, Kelvin Ebiri ya fitar a ranar Litinin domin ya taya tsohon gwamna Peter Odili murnar cika shekara 74.

Ebiri yace Mai girma gwamnan ya yi magana a gidan Peter Odili a garin Fatakwal a jiya.

Kara karanta wannan

An Kafa Kwamitin Mutum 14 da Zai Kawo Karshen Rikicin Atiku da Wike a PDP

Kamar yadda Wike yake fada, manyan PDP sun kawo kansu, suka yi masa alkawarin za su mara baya ga duk wanda ya samu takarar Gwamna a jihar Ribas.

Gwamnan yake cewa bayan sun sha kasa a zaben fitar da gwani na jam’iyyar PDP, sai wadannan mutane suka juya masa baya, saboda ba tayi masu dadi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike.
Nyesom Wike Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

The Cable ta rahoto Wike yana mai cewa dukkanin manyan sun nuna masa su na tare da shi, daga ciki har da Dr Abiye (Sekibo), aka rubuta yarjejeniya.

A cewar Wike, a nan ya nemi su kawo sunan wanda zai zama Gwamnan jihar Ribas bayan shi. Amma kowa ya yi zugun, aka rasa wanda za a ayyana masa.

Daga nan ne ya bukaci duk masu neman kujerar su daga hannuwansu, kusan kowa ya daga hannu illa Sanata Bari Mpigi, wanda ya ji tsoron ya yi biyu-babu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Za Ka Iya Shan Kaye A Zaben 2023, Wike Ya Fada Wa Atiku

Daga nan O.C.J. Okocha ya bada takarda, kowane ya sa hannu da nufin za su goyi bayansa. Wike yace daga baya suka tafi Abuja, su na yi masa zagon kasa.

An rahoto Gwamnan yana cewa wadannan ‘yan siyasa ne suka dage cewa ba za a dauke shi a matsayin ‘dan takarar PDP na mataimakin shugaban kasa ba.

An kai kara da sunan Wike

A farkon makon nan aka samu labari Cosmos Ndukwe yace shi ne ya shigar da kara a kotu, saboda a hana Atiku Abubakar takara, a tsaida Nyesom Wike.

‘Dan siyasar ya shaida cewa ya je kotu ne a dalilin sabawa dokar PDP da aka yi a zaben 2023 domin an tsaida 'Dan Arewa ya nemi shugabancin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel