Kiristocin Jagororin APC 4 da Suka Juyawa Tinubu Baya kan Takarar Musulmi-Musulmi

Kiristocin Jagororin APC 4 da Suka Juyawa Tinubu Baya kan Takarar Musulmi-Musulmi

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya dauko Sanata Kashim Shettima ne a matsayin abokin takararsa
  • Ganin cewa Kashim Shettima Musulmi ne, wannan bai yi wa wasu daga cikin ‘Ya ‘yan APC dadi ba
  • A halin yanzu Kiristoci musamman na Arewacin Najeriya suna nuna rashin goyon bayan wannan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A wannan rahoto, mun tattaro jerin wasu daga cikin kusoshin APC da suka fice daga jam’iyyar, ko suke shirin juyawa Bola Tinubu baya a zaben 2023:

1. Babachir David Lawal

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal yana cikin magoya-bayan Bola Tinubu kafin yanzu, amma ya fito yana tir da ‘dan takaran.

Babachir Lawal ya nuna ba ayi wa Kiristocin Arewa adalci ba, sannan ya soki Kashim Shettima. An ji yana cewa za su yaki APC da addu’a da katin zabe.

Kara karanta wannan

2023: Babachir Lawal Ya Bayyana Yadda Kiristocin Arewa Za Su Yaki Tikitin Musulmi Da Musulmi

2. Yakubu Dogara

Tsohon mataimakin shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Yakubu Dogara ya halarci taron da wasu shugabannin kiristocin APC na Arewa suka shirya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yakubu Dogara ya yi kaca-kaca da APC a kan tsaida Musulmai biyu da tayi a matsayin ‘yan takara. Har an fara rade-radin ‘dan siyasar yana shirin komawa PDP.

Jagororin APC
Dogara, Babachir, Abbo da Bola Tinubu Hoto: Daily Trust, Guardian, BBC, Punch
Asali: UGC

3. Elisha Abbo

Sanata Elisha Abbo bai boye fushinsa a kan yadda Bola Tinubu ya yi watsi da Kiristoci Arewa, ya zabi Musulmi a matsayin abokin takararsa a zaben 2023 ba.

A dalilin wannan Sanatan na Adamawa ya fice daga kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu. Abbo ya nuna ba zai juyawa addininsa baya saboda siyasa ba.

4. Daniel Bwala

Tun a farkon watan nan aka samu labari Daniel Bwala ya fice daga APC da jin labarin Bola Tinubu ya zabi Kashim Shettima ya zama ‘dan takarar mataimakinsa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu : Tinubu Ya Tafka Kuskure Da Ya Dauki Abokin Takara Musulmi – Yakubu Dogara

A karshen watan nan na Yuli, Bwala ya bada sanarwar cewa ya koma goyon bayan Atiku Abubakar, ya jero dalilinsa na goyon bayan ‘dan takaran na PDP.

Ra'ayin Solomon Dalung

Kun samu rahoto tsohon Ministan wasanni da matasa, Solomon Dalung ya soki Jam’iyyar APC da ya bari, saboda ta hana Kirista tikitin takara a 2023.

Dalung yana ganin Bola Tinubu na kokarin amfani da addini wajen ganin ya lashe zabe mai zuwa, amma a cewarsa zai yi wahala APC ta zarce kan mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel