Musulmi-Musulmi: APC na da boyayyar makarkashiya inji Tsohon Ministan Buhari

Musulmi-Musulmi: APC na da boyayyar makarkashiya inji Tsohon Ministan Buhari

  • Solomon Dalung ya soki Jam’iyyar APC da ya bari, saboda ta hana Kirista tikitin takara a 2023
  • Dalung yana ganin Bola Tinubu na kokarin amfani da addini wajen ganin ya lashe zabe mai zuwa
  • Tsohon Ministan wasanni da matasan ya ce hakan zai sa APC ta kara shan wahalar zarcewa a mulki

Solomon Dalung wanda ya taba rike kujerar Ministan wasanni da harkokin matasa a Najeriya, ya zanta da Punch, inda ya tabo batun siyasa da zaben 2023.

Da aka tambayi Solomon Dalung a game da zaben shugaban kasa da za ayi a 2023, ya nuna zai yi wahala jam’iyyar APC ta iya komawa kan karagar mulki.

“Ba na tunanin haka (APC ta ci zabe). Zai zama jan aiki ne mai wahala ga jam’iyyar domin ta barnatar da kaunar da ake yi mata a mulkin shekara bakwai

Kara karanta wannan

2023: Ba Za Mu Bari Mambobin Mu Su Zabi Musulmi Da Musulmi Ba, In Ji Matasan Kungiyar CAN

APC ta kuma kawo abin da zai jawo ba za a zabe ta ba. Da a ce ta tabuka wani abin ne, da 'Yan Najeriya za su yi watsi da batun tikitin musulmi da musulmi".

- Solomon Dalung

Dalung yana ganin cewa tsabagen rashin mutunta addinin mutane ne ya jawo jam’iyyar APC ta tsaida musulmai a matsayin ‘yan takaranta na shugaban kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A wuri na mafi munin abin da APC ta yi shi ne tsaida mabiya addini guda. Sau biyu ana zaben kiristocin Kudu su zama mataimakan Musulman Arewa.”

- Solomon Dalung

Tsohon Ministan Buhari
Shugaba Buhari tare da Solomon Dalung Hoto: www.pulse.ng
Asali: UGC

“Meyasa Bola Tinubu wanda ke takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC zai ce mutane ba za su zabi Musulmin Kudu da Kiristan Arewa a Mataimakinsa ba?”

Akwai abin da ake boyewa

“Dalilin canza abin da aka saba da shi ya fi tikitin ban tsoro, suna boye mana wani abin ne.”

Kara karanta wannan

Da na sha kaye a zabe inda Buhari bai rattaba hannu kan dokar zabe ba - Adeleke

“Abin da nake zargin yana boyewa shi ne, yana biyewa wasu marasa kishin kasa wajen amfani da addini domin yaudarar mutane, su dare kan mulki.”

- Solomon Dalung

Ana yaudara da ci da addini

Dalung ya fadawa Punch, a zahiri wadannan mutane ba addini ya dame su ba, domin da zarar an kafa gwamnati, shugabannin suke ajiye rigar addini.

‘Dan siyasar yake cewa mabiya addini dabam-dabam su na damawa da juna, su na ba juna aure. Dalung ya tafi a kan ra’ayin CAN, ya soki tikitin na APC.

Atiku ya jinjinawa APC

An ji cewa burin Atiku Abubakar shi ne NNPC ya bi sahun kamfanin Aramco da Saudi ta saida, da irinsu Petrobras da Brazil da aka sa a kasuwa.

Bayan Gwamnatin APC ta yi ta sukar maganar saida kamfanin NNPC a 2018, Atiku Abubakar ya ce bayan shekaru hudu an kama hanyar bin dabarunsa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya kaddamar da Mataimaki, ya ce ya dauko wanda za su gyara Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel