Tinubu Ya Tafka Kuskure Da Ya Dauki Abokin Takara Musulmi – Yakubu Dogara

Tinubu Ya Tafka Kuskure Da Ya Dauki Abokin Takara Musulmi – Yakubu Dogara

  • Yakubu Dogara, tsohon kakakin majalisar wakilai, ya yi kaca-kaca da tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da aka dauki musulmi da musulmi.
  • Shugabanin Kristocin Arewa sun gudanar da babban taron a ranar Juma'a a birnin tarayya Abuja
  • Sanata Elisha Abbo da tsohon ministan matasa da wasanni Solomon Dalung suna cikin wadanda suka halarci taron kristocin Arewa

Abuja - Yakubu Dogara, tsohon kakakin majalisar wakilai, ya yi kaca-kaca da tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da aka dauki musulmi da musulmi. Rahoton The Cable

Dogara ya bayyana rashin jin dadinsa ne a ranar Juma’a a wajen taron shugabannin Kiristocin Arewa na jam’iyyar APC.

APC ta fuskanci suka bayan Bola Tinubu, dan takararta na shugaban kasa, ya zabi Kashim Shettima, tsohon gwamnan Borno a matsayin abokin takararsa.

Kara karanta wannan

2023: Babachir Lawal Ya Bayyana Yadda Kiristocin Arewa Za Su Yaki Tikitin Musulmi Da Musulmi

Dogara
Tinubu Ya Tafka Kuskure Da Ya Dauki Abokin Takara Musulmi – Yakubu Dogara foto punch
Asali: UGC

Dogara ya ce maganar banza ne a ce babu wani Kirista da ya isa ya zama abokin takarar Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon kakakin ya ce tikitin zai haifar da rashin hadin kai a jam’iyyar da ma kasa baki daya.

Ya bayyana shawarar Tinubu a matsayin "Tafka babban kuskurei".

Elisha Abbo, sanatan Adamawa mai ci, Solomon Dalung, tsohon ministan matasa da wasanni ne suka halarci taron.

Hukumar Kwastam, NAFDAC, NDLEA sun lalata kwantena 48 na magungunan jabu a Legas

A wani labari kuma, A jiya ne hukumar kwastam ta Najeriya ta jagoranci wasu hukumomin gwamnatin tarayya wajen lalata kwantena 48 na magungunan da aka kama, marasa inganci da na jabu a wurin lalata shara na LAWMA da ke Epe a Legas. Rahotan TheNation

Magungunan da aka lalata kimar su ya kai sama da Naira biliyan daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel