2023: An samu mutumin farko da ya fita daga APC tun da Tinubu ya dauki Musulmi

2023: An samu mutumin farko da ya fita daga APC tun da Tinubu ya dauki Musulmi

  • Jim kadan da tsaida Kashim Shettima, Daniel H. Bwala ya shaidawa Duniya cewa ya rabu da APC
  • Tsohon mai ba APC shawara a kan harkokin shari’a ya yi murabus jiya daga jam’iyya mai mulki
  • Bwala yana ganin abin da ya dace shi ne APC ta tsaida ‘yan takaran da za su hada-kan ‘Yan Najeriya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Tsohon mai ba jam’iyyar APC shawara a kan harkar shari’a, Daniel H. Bwala ya bada sanarwar cewa ya fice daga APC mai mulki.

Daniel H. Bwala ya sanar da hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli 2022.

Masanin shari’ar ya ce ba zai yiwu ya cigaba da zama a jam’iyyar ta APC ba saboda an saki layi daga abin da ya kamata na hada-kan al’umma.

Kara karanta wannan

Bukola Saraki ya tanka shirin Gwamnonin APC na dauke Wike daga PDP

Legit.ng Hausa ta na zargin Bwala ya dauki wannan mataki ne da jin cewa Bola Tinubu ya dauki Kashin Shettima a matsayin abokin takaransa.

Kamar ‘dan takaran shugaban kasar na APC watau Bola Tinubu, shi ma Shettima musulmi ne. Wasu su na ganin ba ayi wa Kiristoci adalci ba.

Sanarwar Daniel Bwala

“A daren yau, ta tabbata cewa na tashi daga zama ‘dan jam’iyyar @OfficialAPCNg, saboda akidu na da imanin da na yi riko da shi da kyau.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“A irin wannan lokaci da muke zaune a tare, kamata ya yi karfinmu da yunkurin ya tafi wajen hada kan mutanenmu.” – Daniel H. Bwala.

Da sakon Bwala wanda a baya yana da kujera a majalisar NWC, za a fahimci yana ganin tikitin Musulmi da Musulmi zai raba kan jama’a ne.

Kafin ya bada sanarwar nan a yammacin Asabar, wani ya tambayi Lauyan a game da matsayinsa tun da Kashim Shettima ya samu tikiti a APC.

Kara karanta wannan

Babu batun hada-kai da NNPP: Obi ya zabi Baba-Ahmed ya zama abokin takara

Da yake magana a shafin Twitter, ‘dan siyasar ya ce a saurari matakin da zai dauka. Ba da dadewa ba sai The Nigerian Lawyer ta fitar da rahoto.

Babu mamaki a samu wanda za su juyawa APC baya saboda wannan zabi da Tinubu ya yi, kamar yadda wasu ke kukan PDP ta ba ‘Dan Arewa tikiti.

Atiku zai dawo gida

A shekaran jiya aka ji labari Bola Tinubu ya dawo Najeriya domin ya yi bikin sallah a gida. Daga nan aka ji ya tsaida abokin takararsa na zaben 2023.

Ganin saura kwana biyar a shirya zaben Gwamna a jihar Osun, ga rikicin cikin gidan PDP bai lafa ba, an ji cewa Atiku Abubakar zai dawo Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel