Ingiza mai kantu: Kungiyar Yarbawa ta zargi Arewa da kullawa Tinubu tuggu a zaben shugaban kasa na 2023

Ingiza mai kantu: Kungiyar Yarbawa ta zargi Arewa da kullawa Tinubu tuggu a zaben shugaban kasa na 2023

  • Wata kungiyar zamantakewa da siyasa ta Yarbawa mai suna Igbimo Apapo Yoruba Lagbaye, ta zargi yan siyasar arewa da shirin fitar da Tinubu daga tseren shugaban kasa na 2023
  • Kungiyar ta yi zargin cewa wasu yan siyasar arewa na shirya munakisan ne bayan kokarinsu na daura Lawan a matsayin dan takarar APC a zaben shugaban kasa na 2023 ya ci tura
  • Ta ce ba za ta lamunci irin tsangwamar siyasa da aka nunawa Obafemi Awolowo da Abiola ba a kan Tinubu

Abuja Wata kungiyar zamantakewa da siyasa ta kudu maso yammacin kasar, wacce aka fi sani da Igbimo Apapo Yoruba Lagbaye, ta yi zargin cewa ana kulla-kulla son fitar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC daga tseren kujerar a 2023.

Kara karanta wannan

Abokin Takara: APC ta Dimauce, Tinubu ya Takaita Lalubensa a Borno, Kano, Kaduna

Kungiyar ta bayyana cewa wasu yan siyasar arewa sun kammala shiri tsaf don tabbatar da ganin cewa Tinubu ya fita daga takarar shugaban kasa na 2023, jaridar Vanguard ta rahoto.

A wani taron da suka gudanar a Abuja, shugaban kungiyar, Aare Omoluabi Oladotun Hassan, ya ce kungiyar na da bayanai abun dogaro kan kulla-kullan na son maimaita abun da aka yiwa Obafemi Awolowo da MKO Abiola don ganin Atiku Abubakar, dan takarar jam’iyyar PDP ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Asiwaju Bola Tinubu
Ingiza mai kantu: Kungiyar Yarbawa ta zargi Arewa da kullawa Tinubu tuggu a zaben shugaban kasa na 2023 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Hakazalika, kungiyar ta yi zargin cewa yan arewan sun yanke shawarar neman hanyar ganin bayan Tinubu ta hannun hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta bayyana cewa sun billo ta nan ne bayan sun ga cewa kokarinsu na tursasa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan a matsayin dan takarar APC bai cimma nasara ba.

Kara karanta wannan

Dogara ne ya fi cancanta ya zama abokin takarar Tinubu – Kungiya ga APC

Hassan ya kuma yi ikirarin cewa sun kaddamar da yaki da Tinubu ta kafofin watsa labarai inda suke amfani da batan takardun karatunsa.

Ya kuma yi gargadin cewa ba za su lamunci duk wani cin amana da aka shirya a kan tsohon gwamnan na jihar Lagas ba.

Vanguard ta nakalto Hassan yana cewa:

“Muna gargadi kan siyasa mai hatsari da masu kishin arewa da masu son kai ke bugawa, da nufin tilastawa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, fita daga tseren don dan takarar shugaban kasa daga arewa a wata jam’iyyar siyasar ya yi nasara.
“Muna da cikakkun bayanai game da ayyukansu na yaudara da kokarin shigo da Alhaji Atiku Abubakar na PDP ta kofar baya da kuma mara masa baya don ya zama shugaban kasa a 2023.
“Kungiyar Yarbawa ta ‘Yoruba Council Worldwide’ na fatan sanar da cewa ba za mu lamunci kowani irin yunkuri na maimata muguntar da aka yiwa Obafemi Awolowo da MKO Abiola ba, wadanda masu kishirwan mulki daga arewa suka bata masu harkar siyasarsu.”

Kara karanta wannan

Da dumi-duminsa: Peter Obi ya ziyarci Gwamna Nyesom Wike a Port Harcourt

Yayin da kungiyar ta gargadi wadanda take zargin da su janye daga kulla abun da zai mayar da kasar Najeriya farfajiyar Arewa, kungiyar ta bayyana kwarin gwiwar cewa Tinubu zai samar da mafita ga tarin matsalolin da Najeriya ke fuskanta.

Zaben 2023: Fitaccen Dattijon Arewa ya soki Atiku da Tinubu, ya yabi Obi da Kwankwaso

A wani labarin, mun ji cewa daya daga cikin manyan yankin Arewacin Najeriya, Ango Abdullahi ya yi fatali da burin manyan ‘yan takaran shugaban kasa na zaben 2023.

Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa Farfesa Ango Abdullahi ya soki burin ‘dan takaran APC, Bola Ahmed Tinubu da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.

A daidai wannan gaba kuma, za a iya cewa Farfesan ya yabi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Peter Obi da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel