Abokin Takara: APC ta Dimauce, Tinubu ya Takaita Lalubensa a Borno, Kano, Kaduna

Abokin Takara: APC ta Dimauce, Tinubu ya Takaita Lalubensa a Borno, Kano, Kaduna

  • 'Dan takarar shugaban kasar jam'iyyar APC, Asiwaju da jam'iyyar na cigaba da shiga cikin rudanin wanda zasu fidda a matsayin abokin tafiyar Bola Ahmed Asiwaju
  • Duk da dai 'dan takarar ya zabi Kabir Ibrahim Masari a matsayin abokin tafiyarsa na wucin gadi, INEC na bukatar ya gabatar da takaimaiman abokin tafiyarsa kafin ranar 15 ga watan Yuli
  • Sai dai, kiristocin Najeriya sun yi fatali da batun tikitin Musulmi da Musulmi da APC ta bada, inda suke ganin hakan wata sigace da za a cire kiristoci daga mulkin kasa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Rudani bisa takamaiman abokin tafiyar 'dan takarar shugaban kasar jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya cigaba da ta'azzara yayin da yake Abuja don cigaba da tuntuba kan lamarin da ya dauki tsawon lokaci yana kawo rudani.

Kara karanta wannan

2023: 'Dan Takarar Gwamna Ya Zakulo Zukekiyar Jarumar Fim a Matsayin Mataimakiyarsa

Tinubu ya dawo Legas a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni bayan ya gana tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi; Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan; gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da sauransu, da basu samu tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar.

Ana sa ran 'dan takarar shugaban kasar jam'iyyar ya bayyana sunan takamaiman abokin tafiyarsa kafin ko ranar 15 ga watan Yuli kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta bada umarni don ya maye gurbin Kabir Ibrahim Masari, wanda ya bayyana a matsayin abokin tafiyarsa na wucin gadi.

Yayin da wa'adin cikar ranar da INEC ta bada ya ke cigaba da karatowa, Tinubu, APC da kungiyar gwamnonin APC na arewa sun cigaba da fuskanta fargaba bisa zabin abokin tafiyar 'dan takarar shugaban kasar, inda ake cigaba da kalubalantar tikitin Musulmi da Musulmi a jam'iyyar mai mulki. Hakan yasa suka cigaba da neman wanda ya dace da tafiyar.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Zanga-zanga ta barke a sakateriyar APC saboda adawa da zabin Tinubu

Masari, wani jagoran APC ne a jihar Katsina, wanda ke aiki da National Institute for Policy and Strategic Studies a Kuru, jihar Fulato.

Dan takarar shugaban kasar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya dauki gwamnan jihar Delta, Dr Ifeanyi Okowa a matsayin abokin tafiyarsa; yayin da 'dan takarar jam'iyyar Labour, Peter Obi ya dauki mai magana da yawun shugaban kasa, Dr Doyin Okupe a matsayin abokin tafiyarsa na wucin gadi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A dayan bangaren, NNPP ta tsaida Ladipo Johnson a matsayin abokin tafiyar Kwankwaso. Har yanzu LP da NNPP na cigaba da ganawa don ganin yadda za su hadu wuri guda, duk da dai basu riga sun gama tsara wanda za su tsayar dan takarar da mataimakin ba tsakanin Obi da Kwankwaso.

Sai dai, zabar wanda zai zama abokin tafiyar Tinubu na cigaba da jawo cece-kuce yayin da kungiyoyi da dama suka ki amincewa da tikitin masu addini guda.

Kara karanta wannan

Ka ji da matsalolin da ke kanka: Martanin Tinubu ga Atiku kan shaguben abokin takara

Daga cikin sunayen da ake tunanin za a dauki abokin tafiyar 'dan takarar na cikin jihohi uku sun hada da tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima da gwamna mai ci na jihar, Farfesa Babagana Zulum. A jihar Kano, gwamna Abdullahi Umar Ganduje na cikin jerin sunayen, yayin da a jihar Kaduna ake tunanin tsaida gwamna Nasir El-Rufai.

Ajomole ya tsaya a kan cewa APC ba zata jure wannan cacar a cikin wannan lokacin tsananin da 'yan takarar jam'iyyun adawa ke kokarin ganin yadda zasu samu tarin kuri'u daga arewa ba.

A cewarsa, "Maganar gaskiya shi ne Asiwaju bai da wani zabi. Yawancin 'yan arewa musulmai ne kuma daukar abokin tafiyar kirista daga arewa ganganci ne wanda zai iya raba masa kuri'u har ya bawa Atiku kafa. Amma idan ya zabi musulmi, za su yi tururuwar kada masa kuri'u."

Har ila yau, kungiyar Christian Reformed church - Nigeria (CRC-N) a ranar Asabar ta yi fatali da batun tikitin Musulmi da Musulmi da APC ta bada.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan jinya a Landan, an sallami tsohon shugaban Najeriya a asibiti

CRC-N synod ta ce Najeriya na da addinai daban-daban kuma bada tikitin Musulmi da Musulmi zai zo da kalubale.

Hakan yazo ne karshen taro na 154 na kungiyar babban Cocin da shugaban cocin, Rabaran Isaiah Jiraoye da babban magatakarda, Rabaran Sagarga Gargea suka rattaba hannu.

Kungiyar ta siffanta hakan da wani shiri don cire kiristoci daga mulkin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel