Zaben 2023: Fitaccen Dattijon Arewa ya soki Atiku da Tinubu, ya yabi Obi da Kwankwaso

Zaben 2023: Fitaccen Dattijon Arewa ya soki Atiku da Tinubu, ya yabi Obi da Kwankwaso

  • Ango Abdullahi ya tofa albarkacinsa a game da manyan ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2023
  • Dattijon ya nuna babu wani abin da Bola Tinubu da Atiku Abubakar za su iya tabukawa a kan mulki
  • Farfesa Ango ya ce Yemi Osinbajo da Mohammed Hayatuddeen za su fi cancanta da shugabanci

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Daya daga cikin manyan yankin Arewacin Najeriya, Ango Abdullahi ya yi fatali da burin manyan ‘yan takaran shugaban kasa na zaben 2023.

Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa Farfesa Ango Abdullahi ya soki burin ‘dan takaran APC, Bola Ahmed Tinubu da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.

A daidai wannan gaba kuma, za a iya cewa Farfesan ya yabi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Peter Obi da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo.

Kwankwaso mutumin kirki ne

Kara karanta wannan

An yi kus-kus: Abin da Bola Tinubu ya shaida wa sanatocin APC a wata ganawar sirri

“Shi (Kwankwaso), mutumin kirki ne, mai karancin shekaru. Tare da mu ya fara siyasa, kuma yana da wayau sosai.”
“Shakka babu, ya gamu da cikas a tafiyar siyasarsa, amma yana cikin masu makomar da ake da su, babu tababa a nan.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Atiku
Atiku da Kwankwaso Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Obi, Osinbajo da Hayatuddeen

An ji tsohon shugaban jami’ar na Ahmadu Bello yana jawabi a game da Peter Obi da Farfesa Yemi Osinbajo wanda bai samu tikitin yin takara a jam'iyyar APC ba.

A PDP kuwa, tsohon ‘dan takaran gwamnan ya ce irinsu Mohammed Hayatuddeen za su fi dacewa da rike Najeriya domin mutum ne wanda ya san aiki.

Ban san Peter Obi ba - Ango

“Abin takaici, ban san Peter Obi sosai ba. Mutum ne mai karancin shekaru, tsohon gwamnan Anambra, kuma ‘dan kasuwa.”

Kara karanta wannan

2023: Mutane za su gamsu idan su ka ji wanda Tinubu zai tafi da shi inji Jigon APC

“Mu na da dandazon ‘yan takara da yawa. Maganar gaskiya akwai mutane irinsu Osinbajo, zai dace, amma ba za a tafi da shi.”

Tinubu da Atiku ba za su iya ba

Sahelian Times ta ce jagoran na kungiyar dattawan Arewa ya dauki lokacinsa ya na mai gargadin ‘Yan Najeriya a kan zaben Atiku Abubakar ko Bola Tinubu.

Ango Abdullahi yake cewa ‘yan takaran na APC da PDP ba za su iya tabuka komai ba, ya ce jama’a su shirya shiga matsala idan waninsu ya lashe zaben 2023.

“Wadanda mu ke da su ba su dace ba."
Ya za a kalli Tinubu da Atiku, ayi tunanin su ne za su yi gyara? Shekaru 25 ko 30 kenan ana damawa da su, me suka yi?”

Hadin kan NNPP da LP

Dazu aka ji labari, jigon NNPP yana cewa Rabiu Kwankwaso za a ba tikitin hadaka, idan har aka hada-kai da 'dan takarar jam’iyyar LP, Peter Obi.

Kara karanta wannan

Uwargidar Najeriyar gobe: Labarin Matan Tinubu, Atiku, Peter Obi da na Kwankwaso

Abdulmumin Jibrin ya ce 'dan takaran na NNPP ne yake da jama’a, da yawan kuri’u da gogewa a siyasa da sanin ilmin lashe zabe fiye da Peter Obi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel