Dogara ne ya fi cancanta ya zama abokin takarar Tinubu – Kungiya ga APC

Dogara ne ya fi cancanta ya zama abokin takarar Tinubu – Kungiya ga APC

  • Wata gamayyar kungiya ta bukaci jam'iyyar APC mai mulki da ta dauki tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara a matsayin abokin takarar Bola Tinubu a zaben 2023
  • Kungiyar ta bayyana cewa Dogara na da dukkanin abun da ake bukata don zama mataimakin shugaban kasa a babban zaben kasar mai zuwa
  • Ta kuma ce hakan zai zama shine adalci da daidaito kasancewar Dogara kirista daga yankin arewacin kasar

Kaduna - Gabannin babban zaben shugaban kasa na 2023, wata gamayyar kungiyar zaman lafiya ta nuna goyon bayanta ga tsohon kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara, inda ta ce shine ya fi cancanta ya zama abokin takarar Bola Tinubu na jam’iyyar All progressives Congress(APC), The Cable ta rahoto.

Da yake martani a wani taron manema labarai a Kaduna, a ranar Asabar, 25 ga watan Yuni, shugaban kungiyar na kasa, Dr. Muhammad Chindo, domin tabbatar da adalci da daidaito, ya kamata wanda za a zaba a matsayin abokin tafiyar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya zama mutum wanda ke da cancantar da ake bukata da gogewar siyasa kamar Dogara.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Zanga-zanga ta barke a sakateriyar APC saboda adawa da zabin Tinubu

Tinubu da Dogara
Dogara ne ya fi cancanta ya zama abokin takarar Tinubu – Kungiya ga APC Hoto: The Cable
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta nakalto Chinco yana cewa:

“Yana da matukar muhimmanci cewa mataimakin shugaban kasa na gaba ya zama kirista da zai iya warware batun da ke da nasaba da addini da tagwayen sharri na kabilanci da bangaranci.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Mun hadu mun yanke shawarar cewa mutumin da ya fi dacewa don rike mukamin mataimakin shugaban kasa na gaba karkashin APC, ba koma bane face Yakubu Dogara, tsohon kakakin majalisar wakilan Najeriya.
“A lokacin da muka zartar da hukuncinmu na daukar Rt.Hon. Yakubu Dogara a matsayin abokin takarar Asiwaju Bola Tinubu, kungiyar ta yi la’akari da wasu abubuwa: A matsayinsa na dan majalisar wakilai ta tarayya kuma kakakin majalisar wakilai daga 2007 har sai da ya amince ya sauka don kansa, Dogara na da abin da ake bukata na gogewar siyasa da ilimi, fiye da suk wanda za a uya gabatarwa a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Zulum ne ya fi cancanta ya zama abokin takarar Tinubu, in ji kungiyar masu ruwa da tsaki na APC

“Rt. Hon. Yakubu Dogara dan siyasa ne nagartacce wanda al’ummar mazabarsa suka gwada shi kuma suka amince da shi, wanda ya samu daukaka da alfarmar zabe sau hudu a jere.
“Yakubu ya kasance mai dinke baraka wanda ke da tausayi, son ci gaba, da son mutane. A kullun yana samun yarda da amincewar al’ummar mazabarsa ta Dass/Tafawa Balewa/Bigoro, wadda ta kunshi mutane daban-daban wadanda suke da bambancin addini da kabila.

2023: Osinbajo na fuskantar matsin lamba don sake shiga tseren shugaban kasa, an nemi ya hade da Kwankwaso

A wani labarin kuma, mun ji cewa cewa ana kulla-kulla don hada kawance tsakanin jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) da sansanin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a kokarin ganin ya dawo tseren shugaban kasa na 2023.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa majiyoyi a sansanonin biyu sun dage cewa akwai shawarwari masu karfi da ke gudana dangane da yiwuwar samun tikitin Osinbajo/Kwankwaso a karkashin inuwar jam’iyyar NNPP.

Kara karanta wannan

Dangin gwamna: Muhimman abubuwa 8 da baku sani ba game da abokin takarar Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel