Jigon siyasa: Cikin APC da PDP ya duri ruwa ganin yadda Peter Obi ya samu karbuwa

Jigon siyasa: Cikin APC da PDP ya duri ruwa ganin yadda Peter Obi ya samu karbuwa

  • Peter Obi na sanya rashin barci a idon jiga-jigan siyasa a Najeriya a cewar Sanata Victor Umeh, tsohon jigon APGA
  • Umeh ya ce yakin neman zaben Obi ya dauki salo mai kyau, lamarin da ya jefa firgici a sansanin APC da PDP
  • Peter Obi ya koma jam’iyyar Labour ne makonnin da suka gabata, kuma hakan ya kawo juyin juya hali a siyasar Najeriya

Awka, jihar Anambra – Sanata Victor Umeh ya bayyana cewa gungun jama’a da ke kaunar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Mista Peter Obi, ya zama abin damuwa ga jam’iyyar APC mai mulki da kuma babbar jam’iyyar adawa, PDP.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Umeh ya bayyana hakan ne a wani sashe na tattaunawa da wasu ‘yan kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya, a Awka, babban birnin jihar Anambra a ranar Talata, 21 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

PDP ta ragu: Sanatan PDP ya sauya sheka, ya bi sahun Peter Obi a jam'iyyar Labour

Peter Obi ya samu karbuwa, PDP da APC sun razana
Jigon siyasa: Cikon APC da PDP ya duri ruwa ganin yadda Peter Obi ya samu karbuwa | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Yace:

“Goyon bayan da ‘yan Najeriya ke baiwa tsohon gwamnan jihar Anambra kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Mista Peter Obi, yana ba ‘ya’yan jam’iyyar APC, PDP, da sauran jam’iyyu tsoro sosai gabanin zaben 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"APC, PDP, da sauran jam'iyyun siyasa na tsoron Peter Obi saboda kudurinsa na korar talauci da iya sarrafa albarkatun kasa."

Umeh wanda tsohon shugaban jam’iyyar APGA ne ya ce Obi ya fice daga PDP ne saboda babban makirci da zagon kasa da ake kullawa kabilar Igbo da daukacin shiyyar kudu maso gabas a yunkurinsu na neman shugabancin kasar.

Ya kara da cewa wannan ta’asa na hana yankin kudu maso gabas da Igbo shugabancin kasa da manyan jam’iyyu biyun suka yi sam ba a abin amincewa bane kuma ya sabawa ka’ida da na tsarin karba-karba.

Kara karanta wannan

Majan LP da NNPP: Sai dai Peter ya zama mataimaki, Kwankwaso shugaba, inji NNPP

Kalamansa:

“Idan ka kalli zaben fidda gwani na shugaban kasa na APC da PDP, da ‘yan kabilar Igbo kashe kawunansu da kunya ba dan Peter Obi da jam’iyyar Labour ba.
“’Yan Najeriya na kowane tsagi suna ta gangami ga manufar Peter Obi. Dole ne ‘yan Najeriya su nuna himma da kauna. Abin da ke faruwa na Allah ne. Obi tambari ne mai zafi.
“Muna kira ga ‘yan Najeriya da su yi gangamin ga Peter Obi. Peter Obi ya tsaya tsayin daka don amfanar Najeriya da al'ummarta. Fatan da ‘yan Najeriya ke bukata shi ne Peter Obi, ko da a cikin yalwar arziki ne ba zai iya barnata albarkatun kasa ba."

Matasa suke tsoro, ba Peter Obi ba - Peter P-Square ya bayyana

A nasa bangaren, mawaki Peter Okoye na tawagar P-Square ya bayyana cewa manyan jam’iyyun siyasa ba sa tsoron Obi, sai dai kawai a ce matasan Najeriya na mara masa baya.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Zanga-zanga ta barke a sakateriyar APC saboda adawa da zabin Tinubu

Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa:

“Ba sa tsoron Peter Obi, suna tsoron ku, matasa, kuna tunatar da su #Sorosoke, #EndSars, kuna tuna musu rauninsu wanda suke tsoron su sani. Don haka ku tsaya kan layi kar ku karaya! Amsar kawai ita ce PVCn ku."

Jigon APC: Sanatocin Mu 22 Suna Barazanar Komawa Jam'iyyar PDP, Dole Mu Dauki Mataki

A wani labarin, akwai yiwuwar a kalla sanatocin jam'iyyar APC mai mulki za su fice daga jam'iyyar su koma babban jam'iyyar hamayya ta PDP, a cewar Femi Fani-Kayode.

A cewar sanarwar da ya fitar ta shafinsa na Twitter a ranar Laraba, Sanatocin suna barazanar za su fice daga jam'iyyar saboda an hana su tikitin sake takarar komawa majalisar.

Kalamansa: "Abin ba wasa bane kuma dole a dauki mataki kansa. Mutane da dama sun damu kuma muna kira ga shugabanmu na kasa da sakatare su tuntube su. Ba zai yiwu mu bari su fice ba."

Kara karanta wannan

Ba dai a 2023 ba: Babangida Aliyu ya sha Peter Obi, ya ce ba zai yi mulki ba sai 2027 ko 2031

Asali: Legit.ng

Online view pixel