PDP ta ragu: Sanatan PDP ya sauya sheka, ya bi sahun Peter Obi a jam'iyyar Labour

PDP ta ragu: Sanatan PDP ya sauya sheka, ya bi sahun Peter Obi a jam'iyyar Labour

  • A karshe dai jam'iyyar Labour ta samu wakilci a babban zauren majalisar dokokin Najeriya yayin da wani sanata ya sauya sheka
  • Sanata Ezenwa Francis Onyewuchi mai wakiltar Imo ta Gabas a kujerar Sanata, ya koma jam'iyyar Labour a hukumance
  • A hankali jam’iyyar Labour tana samun karbuwa Najeriya, musamman ganin Peter Obi a matsayin dan takararta na shugaban kasa

Sanata Ezenwa Francis Onyewuchi mai wakiltar kujerar Sanata a Imo ta Gabas, wanda aka zaba a jam'iyyar PDP ya koma jam'iyyar Labour a hukumance.

'Yan majalisu da sanatoci da dama a kasar nan sun sauya sheka daga jam'iyyun siyasarsu zuwa wsau saboda wasu dalilai a shekarar nan.

Sanatan PDP ya hakura ya koma jam'iyyar Labour
Da dumi-dumi: Sanatan PDP ya sauya sheka, ya bi sahun Peter Obi a jam'iyyar Labour | Hoto: @EzenwaOnyewuchi
Asali: UGC

A wata wasika da ya aike wa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, Sanata Onyewuchi ya ce:

Kara karanta wannan

Da dumi-duminsa: Peter Obi ya ziyarci Gwamna Nyesom Wike a Port Harcourt

“Ina so in sanar da shugaban majalisa da jiga-jigan ‘yan majalisar dattawa kan ficewa ta daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar Labour.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Wannan ya biyo bayan shawarwarin da suka dace da iyalina, mazaba da magoya bayana.
"Hakan zai ba ni damar shiga harkar neman kafa sabuwar Najeriya."

Ficewar sanatan a yau ya kawo adadin 'yan jam'iyyu marasa rinjaye zuwa 43, Legit.ng ta tattaro.

Kananan jam’iyyu a majalisar dattawa a yanzu sun kai biyar ya zuwa ranar Laraba 22 ga watan Yuni. Onyewuchi shine dan majalisar dattawa na farko na jam’iyyar Labour a majalisar dattawa ta 9.

Onyewuchi ya tabbatar da sauya shekarsa ta shafin Twitter

A shafinsa na Twitter, sanatan ya tabbatar da cewa ya sauya sheka, yayin da ya yada hoto allon talla mai dauke tutar jam'iyyar Labour da kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar; Peter Obi.

Kara karanta wannan

AbdulMumini Jibrin ya daura hoton Kwankwaso ya 'badda kama, tambar Obama

A kalamansa:

“Mai yiwuwa ne samar da sabuwar Najeriya.”

Koma baya: APC ta gigice, jiga-jiganta a Katsina, Sokoto da Bauchi sun sauya sheka

A wani labarin, wasu jiga-jigan jam’iyyar APC guda shida da suka hada da ‘yan majalisa da kuma tsohon mataimakin gwamna sun fice daga jam’iyyar tare da sauya sheka zuwa wasu jam’iyyun siyasa daban-daban a jihar Bauchi.

Ficewar dai babbar illa ce ga burin jam’iyyar na ganin bayan jam’iyyar PDP mai mulki a jihar a zaben gwamna na 2023. Gwamna mai ci Bala Mohammed na neman wa’adinsa na biyu kuma na karshe a matsayin gwamna.

Tashin hankalin ficewa daga jam’iyyar APC ya tsallaka jihar Bauchi. A wasu jahohin Arewacin kasar nan ma ‘yan jam’iyyar sun koka kan yawan ficewa da shiga wasu jam’iyyun siyasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel