Jigon APC: Sanatocin Mu 22 Suna Barazanar Komawa Jam'iyyar PDP, Dole Mu Dauki Mataki

Jigon APC: Sanatocin Mu 22 Suna Barazanar Komawa Jam'iyyar PDP, Dole Mu Dauki Mataki

  • Jigon a jam'iyyar APC, Femi Fani-Kayode ya bayyana cewa akwai yiwuwar sanatocin jam'iyyar 22 su koma Jam'iyyar PDP
  • Fani-Kayode ya bayyana hakan ne cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, yana mai shawartar shugabannin jam'iyyar su tuntubi sanatocin
  • Dama a yau Laraba shugaban majalisar dattawa Sanata Abdullahi Adamu ya gana da sanatocin na jam'iyyar APC ya kuma ce ya damu da fita jam'iyyar da wasu mambobin suka yi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Akwai yiwuwar a kalla sanatocin jam'iyyar APC mai mulki za su fice daga jam'iyyar su koma babban jam'iyyar hamayya ta PDP, a cewar Femi Fani-Kayode.

A cewar sanarwar da ya fitar ta shafinsa na Twitter a ranar Laraba, Sanatocin suna barazanar za su fice daga jam'iyyar saboda an hana su tikitin sake takarar komawa majalisar.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Adamu Da Sanatocin APC Sunyi Taro, An Dauki Matakan Dakile Ficewar Mambobin Jam'iyyar

Femi Fani-Kayode.
Dole Mu Zage Damtse: Sanatocin APC 22 Suna Shirin Komawa PDP, In Ji Fani-Kayode. @Vangaurdngr.
Asali: Twitter

Kalamansa:

"Abin ba wasa bane kuma dole a dauki mataki kansa. Mutane da dama sun damu kuma muna kira ga shugabanmu na kasa da sakatare su tuntube su. Ba zai yiwu mu bari su fice ba."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bangarensa, Shugaban jam'iyyar na APC na kasa, Adamu Abdullahi ya gana da sanatocin jam'iyyar a ranar Laraba.

Adamu ya kuma gana da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan kafin taronsa da sanatocin a majalisar.

An gano cewa adadin sanatocin na APC yanzu ya koma 62, saboda wadanda suka gaza samun tikitin sake yin takara.

A baya-bayan nan, sanatoci biyu daga Jihohin Imo da Bauchi sun sanar da ficewarsu daga APC da PDP yayin zaman majalisar.

Sanatoci sun hada da Dauda Jika mai wakiltar Bauchi Central da aka zaba a karkashin APC; da Ezenwa Francis Onyewuchi mai wakiltar Imo East da aka zaba karkashin PDP.

Kara karanta wannan

PDP ta ragu: Sanatan PDP ya sauya sheka, ya bi sahun Peter Obi a jam'iyyar Labour

A wasiku daban-daban da suka tura wa Lawan, Sanatocin sun sanar da murabus dinsu daga APC da PDP, don shiga Labour Party da NNPP.

Sanatan APC Ya Saka Wa Daliget Da Kujerun Hajji Bayan Sun Dawo Masa Da Kudinsa Don Ba Su Zabe Shi Ba

A wani rahoton, Sanata Smart Adeyemi wanda ya wakilci Kogi West a Majalisar Tarayya, ya bada kujerun Hajji ga mutum biyar cikin daligets din da ya bawa kudi amma ba su zabe shi ba a zaben fidda gwani na APC.

Adeyemi ya rasa damar komawa majalisar ne a yayin da ya samu kuri'u 43 a zaben fidda gwanin, hakan yasa ya zo na uku.

Sunday Karimi, wanda ya samu tikitin jam'iyyar ya samu kuri'u 288, yayin da Muyiwa Aina wanda ya zo na biyu ya samu kuri'u 73.

Asali: Legit.ng

Online view pixel