Majan LP da NNPP: Sai dai Peter ya zama mataimaki, Kwankwaso shugaba, inji NNPP

Majan LP da NNPP: Sai dai Peter ya zama mataimaki, Kwankwaso shugaba, inji NNPP

  • Wani sabon al’amari ya kunno kai yayin da ake ci gaba da kokarin ganin an yi maja tsakanin jam’iyyar NNPP da Labour Party
  • A yanzu haka, NNPP ta ce hanya guda da za a iya samun maslaha tsakanin jam’iyyun biyu shine Peter Obi ya hakura ya barwa Kwankwaso matsayin shugaban kasa
  • Tun farko dai tsohon gwamnan na jihar Kano ya tabbatar da cewa ana kan tattaunawa tsakaninsu da jam’iyyar Obi

AbujaKakakin kungiyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Mista Major Agni, ya bayyana cewa sharadi guda na yin maja tsakaninsu da Labour Party (LP) shine cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Peter Obi ya yarda ya zama abokin takarar Rabiu Musa Kwankwaso.

Da yake jawabi a talbijin din Arise a ranar Talata, 21 ga watan Yuni, kakakin na NNPP ya bayyana cewa Kwankwaso ne ya yi nasara cikin yan takarar shugaban kasa 18 a zaben da suka yi kuma har yanzu shine suka fi so ya zama shugaban kasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Ba ku da tsari: Dan kashenin Jonathan ya fice daga PDP, ya caccaki tsarin jam'iyyar na 2023

Peter Obi and Kwankwaso
Majan LP da NNPP: Sai dai Peter ya zama mataimaki, Kwankwaso shugaba, inji NNPP Hoto: Change Nigeria
Asali: UGC

Ya dage cewa jam’iyyar na ci gaba da samun kiraye-kiraye cewa lallai kada Kwankwaso ya janyewa Obi, yana mai cewa maslaha daya shine Obi ya yarda ya zama mataimakin Kwankwaso.

Ya bayyana cewa Kwankwaso ya sauya rayukan talakawa, yana mai cewa akwai bukatar a barshi ya jagoranci yarjejeniyar LP/NNPP, jaridar Thisday ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Muna ci gaba da samun kiraye-kiraye. Mutane da dama sun kira suna fadin cewa, a’a, ba za mu yarda da wannan ba. Wannan shine kawai abun da muke so ku cimma matsaya a kai cewa Peter ne zai zama mataimaki.”

Agbo ya jadadda cewa koda dai Obi mutumin kirki ne wanda shima ya yi namijin kokari, ba zai yiwu ace ya yi jagoranci ba a duk yarjejeniyar da za a cimma game da zaben shugaban kasar 2023.

Ya kuma karyata cewa Kwankwaso na da karfi ne a iya Kano da Jigawa, yana mai cewa duk wanda ya yarda da hakan toh an batar da shi ne, ya kuma ce jam’iyyar ta shafe tsawon shekaru 21.

Kara karanta wannan

Babu Wannan Maganar: NNPP Ta Karyata Rade-Radin Kwankwaso Ya Zama Mataimakin Obi

Ya kuma yi watsi da rade-radin cewa jam’iyyar NNPP/LP ta shirya kawance ne kawai don ruguza jam’iyya All Progressives Congress (APC) mai mulki da jam’iyyar adawa ta PDP, yana mai cewa jam’iyyun a shirye suke su karbi mulki.

Kwankwaso ya tabbatar da cewar suna kan tattaunawa da Peter Obi don hada gwiwar NNPP da LP

A baya mun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Sanata Rabiu Kwankwaso, a ranar Asabar, ya tabbatar da cewar jam’iyyarsa na kan tattaunawa da jam’iyyar Labour Party da dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi.

Ya ce suna tattaunawa ne kan yiwuwar yin maja a babban zaben shugaban kasa ta 2023 mai zuwa.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata hira da sashin Hausa na BBC a ranar Asabar, 18 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel