2023: Yadda ƴaƴan CJN Tanko 2 suka samu tikitin takarar sanatoci a Bauchi

2023: Yadda ƴaƴan CJN Tanko 2 suka samu tikitin takarar sanatoci a Bauchi

  • 'Ya'ya biyu na alkalin alkalai Ibrahim Tanko sun samu tiket na takarar kujerar sanatoci daga jihar Bauchi
  • 'Daya daga cikin 'ya'yan ya samu a karkashin jam'iyyar APC yayin da 'dan uwansa ya samu a PDP duk a jihar Bauchi
  • Siraj Tanko ya lallasa Sanata Bulkachuwa da wasu mutum 2, yayin da Sani Tanko ya yi nasara babu abokin hamayya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Bauchi - 'Ya'ya biyu na shugaban alkalan Najeriya, Jastis Ibrahim Tanko, sun samu tikitin takarar kujerar sanatoci a zaben 2023 a jihar Bauchi.

Daya daga cikin 'ya'yan, Siraj Ibrahim Tanko, ya samu nasarar caraf da tikitin a karkashin jam'iyyar APC na Bauchi ta arewa, Daily Trust ta ruwaito.

2023: Yadda ƴaƴan CJN Tanko 2 suka samu tikitin takarar sanatoci a Bauchi
2023: Yadda ƴaƴan CJN Tanko 2 suka samu tikitin takarar sanatoci a Bauchi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya lallasa 'yan takara biyu da suka hada da Sanata mai wakiltar mazabar, Sanata Adamu Bulkachuwa.

Kara karanta wannan

Mutuwar yawa: Duka Sanatoci 3 sun sha kasa a zaben fitar da gwanin jam’iyyar APC a jiha 1

Yayin da Siraj ya samu kuri'u 189, Imba, babban abokin adawarsa ya samu 177 yayin da Bulkachuwa bai tashi da ko kuri'a daya ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

'Dayan 'dan CJN, Sani Ibrahim Tanko, ya yi nasara ne a jam'iyyar PDP a mazabar Shirya Giafe inda zai wakilce su a majalisar wakilai.

Ba kamar 'dan uwansa ba, Sani ya yi nasara ba tare da abokin adawa ko daya ba.

Gwamna Wike: Da Na So, Da Na Tarwatsa Jam'iyyar PDP a Daren Asabar, Hakuri Kawai Nayi

A wani labari na daban, Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers a ranar Litinin ya ce da ya so, da ya tarwatsa jam'iyyar PDP a ranar Asabar yayin zaben fidda dan takarar shugabancin kasa a ranar Asabar, amma sai bai yi hakan ba. An yi zaben fidda dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar domin zaben 2023 mai zuwa.

Kara karanta wannan

APC: Dan majalisan Arewa da ake zargi da badakalar kudin Korona ya rasa tikitin tazarce

"Da na so tarwatsa taron, da na yi hakan kuma na sanar da su. Akwai mutanen da za ka yi zaton 'yan Adam ne, amma ba mutane ba ne," yace.

Premium Times ta rahoto cewa, Wike ya sanar da hakan a wani biki da aka shirya a Fatakwal domin taya shi murnar dawowa gida daga zaben fidda gwanin inda Atiku Abubakar ya lallasa shi.

"Ban taba ganin inda mutane ke saba doka ba da tsarika. Wani ya yi magana, a wannan lokacin ne kadai ya ke magana kan cewa ya janye. Ba a kira shi ba," Gwamnan Rivers ya fada yayin da ya ke nufi da gwamnan jihar Sokoto kuma dan takara, Aminu Tambuwal, wanda ya janye daga takarar kuma ya bukaci magoya bayansa da su zabi Atiku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel