Mutuwar yawa: Duka Sanatoci 3 sun sha kasa a zaben fitar da gwanin jam’iyyar APC a jiha 1

Mutuwar yawa: Duka Sanatoci 3 sun sha kasa a zaben fitar da gwanin jam’iyyar APC a jiha 1

  • Muhammad Adamu Bulkachuwa ya yi mummunar faduwa a zaben fitar da gwani a jihar Bauchi
  • Sanatan bai samu kuri’a ko daya a zaben tsaida ‘dan takarar jam’iyyar APC a Arewacin Bauchi ba
  • Halliru Dauda Jika da Lawal Yahaya Gumau ba za su yi wa APC takara a 2023 ba, sun sha kashi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Bauchi - Duka Sanatocin jihar Bauchi ba za su yi takara a babban zabe da za ayi a 2023 ba. Premium Times ta ce a cikinsu, babu wanda ya samu tikiti.

Abin da ya faru a irinsu jihohin Katsina da Jigawa shi ne ya faru a Bauchi, babu wani Sanata da ke kan mulki da ya iya samun nasara a zaben fitar da gwani.

Muhammad Adamu Bulkachuwa wanda ke wakiltar mazabar Arewacin Bauchi a majalisar dattawa bai samu kuri’a ko daya a zaben fitar da ‘dan takara ba.

Kara karanta wannan

APC tayi zazzaga a jihar Arewa, fitattun ‘Yan Majalisa 7 za su rasa kujerunsu a 2023

Siraj Tanko mai kuri’a 189 a zaben na APC ya yi galaba kan Sanata Muhammad Adamu Bulkachuwa.

An gwabza a Bauchi ta Arewa

Sauran wadanda suka nemi tikitin Sanata a yankin a karkashin jam’iyyar APC su ne; Ibrahim Baba, Sule Katagun, Ladan Yusuf, Safiya Dass da Ibrahim Zailani.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton ya nuna Ibrahim Baba ya samu kuri’u 177, Katagum ya samu 1, Yusuf ya samu kuri’u hudu. Safiya Dass da Zailani ba su samu ko kuri’a daya a zaben ba.

Zaben Sanatan Bauchi
Buhari yana taya APC kamfe a Bauchi Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

Yankin Bauchi ta tsakiya

A yankin Bauchi ta tsakiya, Uba Ahmed Nana ne ya samu takara bayan ya lashe kuri’u 238. Wanda ya zo na biyu shi ne Sanata Isah Hamma Misau mai kuri’a 75.

Na uku a wannan shiyyar shi ne Abubakar Shehu, Uba Nana ya ba Shehu ratar kuri’u har 220.

Kara karanta wannan

Yadda duka Sanatocin Katsina 3 su ka rasa tikitin tazarce a karkashin Jam’iyyar APC

Sanatan da yake rike da wannan kujera shi ne Halliru Dauda Jika wanda ya je neman takarar gwamna, a karshe shi ma ya sha kashi wajen Sadiq Baba Abubakar.

Zaben APC a Bauchi ta Kudu

Shi ma Sanatan Bauchi ta kudu watau Lawal Yahaya Gumau ya rasa zabensa da tazara mara yawa. Gumau ya samu kuri’a 182, ba zai rikewa APC tuta a 2023 ba.

Shehu Buba Umar wanda ya samu takara a jam’iyyar mai adawa a Bauchi ya samu kuri’a 186. A zabe mai zuwa na 2023, za a ga wasu sababbin fuskoki ne daga jihar.

APC ta yi bari a Katsina

A baya kun ji labari cewa jam’iyyar APC mai mulki ta canza wadanda za su yi mata takarar Sanata a duka bangarorin da ke jihar Katsina a zabe mai zuwa.

Hon. Nasir Zangon Daura zai nemi Sanata a shiyyar Daura, Muntari Dan Dutse ya tika Sanata mai-ci, Bello Mandiya da kasa, haka zalika an doke Kabiru Barkiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel